Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Kokarin da Tinubu Ke Yi domin Rage Tsadar Rayuwa

Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Kokarin da Tinubu Ke Yi domin Rage Tsadar Rayuwa

  • Gwamnatin tarayya ta hannun ministan sadarwa da wayar da kan jama'a ta yi tsokaci kan tsadar rayuwa a Najeriya
  • Mohammed Idris ya jaddada cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ƙoƙarin domin ganin ya rage raɗaɗin da ƴan Najeriya ke sha
  • Ministan ya kuma bayyana cewa shugaban ƙasan ya ɗauki matakin tsuke bakin aljihun gwamnati domin rage kuɗin da ake kashewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya yi magana kan tsadar rayuwa a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Ministan ya nanata ƙudirin Shugaba Tinubu na rage raɗaɗin tattalin arziƙin da ƴan Najeriya ke fuskanta, musamman saboda cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya fadi abin da ya sani kan halin da 'yan Najeriya suke ciki

Tinubu na kokari kan tsadar rayuwa
Gwamnatin tarayya ta ce Tinubu na kokarin rage tsadar rayuwa Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa ministan ya bayyana hakan ne a shirin Hannu da Yawa na gidan rediyon tarayya (FRCN).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed Idris ya ce tallafin man fetur ya fi amfanar wasu tsirarin mutane fiye da ɗumbin jama'an da aka samar da shi domin su.

Wane ƙoƙari Tinubu ke yi kan tsadar rayuwa?

Ministan ya tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu na aiki tuƙuru wajen ƙoƙarin ganin tattalin arziƙin ƙasar nan ya samu daidaito.

Ya ƙara da cewa shugaba Tinubu ya buƙaci ministoci su rage kuɗin gwamnati da suke kashewa ta hanyar taƙaita yawan ababen hawa da ƴan rakiya a tafiye-tafiyensu.

Ya bayyana cewa waɗannan matakan tsuke bakin aljihun gwamnati, duk da cewa sun yi kaɗan, za su yi tasiri sosai.

Dangane da batun tsaro kuwa, Mohammed Idris ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu na ci gaba da samar da kayan aiki ga hukumomin tsaro da inganta jin ɗaɗin jami'an tsaro

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi lokacin kawo karshen matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya

Tinubu ya ba ƴan Najeriya shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta yi kira ga ƴan Najeriya su rungumi noma ido rufe domin magance tashin farashin kayan abinci da ake fuskanta a ƙasar nan.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ne ya yi wannan kiran yayin taron da ya yi da wata kungiyar editocin yanar gizo ta ACOE a Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng