Tsadar Rayuwa: Gwamna a Arewa Ya Amince a Ba Ma'aikata Tallafin Kudi na Wata 3

Tsadar Rayuwa: Gwamna a Arewa Ya Amince a Ba Ma'aikata Tallafin Kudi na Wata 3

  • Gwamnatin Kwara ta sanar da shirinta na ba ma'aikatan jihar da ma na kananan hukumomi alawus na watanni uku
  • Kwamishiniyar kudi ta jihar, Hauwa Nuru ta bayyana cewa ma'aikata za su samu tallafin kudin daga Oktoba zuwa Disamba
  • A cewar kwamishiniyar, Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya amince da ba da tallafin saboda rage radadin tsadar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya amince a bai wa ma'aikatan jiharsa ciki har da na kananan hukumomi tallafin kudi.

An ce gwamnan ya amince alawus din da za a bai wa ma'aikatan ya yi daidai da kudin 'PAYE' da ake biyan kowanne ma'aikaci a jihar na wata-wata.

Kara karanta wannan

Kano: Likitoci sun dauki zafi, sun ba gwamna awanni 48 ya kori kwamishiniyarsa

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq zai ba ma'aikatan jihar Kwara tallafin kudi
Ma'aikata a jihar Kwara za su samu tallafin kudi na watanni 3. Hoto: @followKWSG
Asali: Facebook

Gwamnatin Kwara za ta ba da alawus

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kwamishiniyar kudi ta jihar, Hauwa Nuru wadda aka wallafa a shafin gwamnatin Kwara na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hauwa Nuru ta bayyana cewa, wannan shirin ba ma'aikata tallafin kudin zai gudana na tsawon watanni uku daga Oktoba zuwa Disamba.

Kwamishiniyar ta ce wannan tallafin zai taimaka wajen rage tasirin sauyin da aka samu a harajin PAYE da ake cirewa bayan bullo da sabon mafi karancin albashi.

An gargadi ma'aikatan jihar Kwara

Ta bayyana tallafin a matsayin abin da ya wajaba domin taimakawa ma’aikata yayin da suke kokarin sabawa da sabon tsarin PAYE da aka aiwatar bisa ga dokar harajin shiga na sirri.

"Biyan tallafin kudin zai fara aiki daga watan Oktoba har zuwa Disambar 2024. Wannan mataki ne da mai girma gwamna ya dauka domin tallafawa ma'aikata."

Kara karanta wannan

Gwamna ya kakaba harajin N40,000 kan mafi ƙarancin albashi? Fintiri ya yi martani

- A cewar Hauwa Nuru.

Ta kuma bukaci ma’aikata da su tabbatar sun yi rajista da hukumar rajistar mazauna jihar Kwara (KWSRRA), inda ta ce wadanda ba su da rajista ba za su samu alawus din ba.

Gwamna ya amince da karin albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da sabon mafi karancin albashi na N70,000.

Kwamishiniyar Kudi, Hauwa Nuru, ta ce za a fara aiwatar da sabon mafi karancin albashin ga daukacin ma’aikatan jihar Kwara daga Oktoba 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.