Kalubale ga Arewa: Yadda Farfesa Maqary ke shige da fice don kubutar da yaran da aka kulle a Abuja

Kalubale ga Arewa: Yadda Farfesa Maqary ke shige da fice don kubutar da yaran da aka kulle a Abuja

  • Bayan fitowar hotuna da bidiyo na yara kananan da aka gurfanar a kotu bisa zargin sun ci amanar kasa, limamin Abuja ya dauki mataki
  • Farfesa Maqary ya dauki N1,000,000 ya bayar don tabbatar da an sayi magani da abinci ga yaran da aka garkame ba tare da bin ka’ida ba
  • An zargi kananan yara da cin amanar kasa duk da cewa sun fito zanga-zangar nuna kiyayyarsu ga wahalar da gwamnatin Najeriya ke ba ‘yan kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - A wani yanayi mai ban tausayi, Farfesa Ibrahim Maqary ya ba da tallafin kudi N1,000,000 domin tabbatar da kubutar da kananan yaran da ‘yan sanda suka gurfanar a kotun tarayya da ke Abuja.

A makon da ya gabata ne wasu hotuna masu tada hankali suka nuna yadda ‘yan sanda suka gurfanar da kananan yara a gaban kotu bisa zargin cin amanar kasa.

Kara karanta wannan

Limamin masallacin Abuja, Maqary ya yi magana mai zafi sakamakon kama 'yan yara

Matsayar Maqary kan kama kananan yara
Maqary ya ba da tallafi ga yara | Hoto: Prof. Ibrahim Maqari
Asali: Facebook

A cewar rahotanni, an kama yaran ne masu kananan shekaru a lokacin zanga-zangar lumana ta kira ga hambarar da mulkin Tinubu da aka yi a watan Agustan bana.

Zargin da ake yiwa kananan yaran

A cewar lauyoyin gwamnati, an ce ana zargin yaran ne da cin amanar kasata hanyar daga tutar kasar waje tare da kira ga sojoji su hambarar da Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kotun ne aka samu wasu yara suka fadi saboda tsananin yunwa da kuma tsawon ajiye su da aka yi a magarkama tare da ‘yan ta’adda.

A zaman kotu, an ba da belin yaran tare da bayyana adadin kudaden da za su biya, amma aka samu tasgaro duba da yawan kudin da aka shata a matsayin beli.

Maqary ya sa baki a lamarin yaran

A nasa bangaren, limamin babban masallacin kasa da ke Abuja, Ibrahim Maqary ya shiga tashin hankali, inda ya bayyana aniyarsa ta tabbatar da an kubutar da yaran.

Kara karanta wannan

Bayan suka ta ko ina, gwamnatin Tinubu ta shiga lamarin yara 76 da aka kai kotu

Ya ba da tallafin kudi, ya kuma bukaci manyan Arewa da su gaggauta sanya baki wajen tabbatar da yiwa kananan yaran adalci.

A halin da ake ciki, lauya Abba Hikima da Hamza Nuhu Dantani da ke kan gaba a kare yaran a kotu suna ta kokarin yiwa yaran magani tare da tabbatar da sun fito lafiya.

Matsayar Maqary kan tsare 'yan yara

A tun farko, Farfesa Ibrahim Maqary ya yi magana bayan ganin bidiyon kananan yaran da aka gurfanar a wata kotun tarayya.

Limamin babban masallaci na kasa da ke garin Abuja ya yi tir da yadda ‘dan adam yake wulakanta bayin Allah a duniyar yau.

A wani bidiyo da wani Meeqdad Mujtaba ya wallafa a dandalin Facebook, an ji malamin ya na tir da cin zarafin kananan yara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.