Rusau Ba Bisa Ka’ida Ba: Yadda Wike Ya Rushe Gidaje 100 a Abuja, Ya Jawo Asarar N200bn Nan Take

Rusau Ba Bisa Ka’ida Ba: Yadda Wike Ya Rushe Gidaje 100 a Abuja, Ya Jawo Asarar N200bn Nan Take

  • Kungiyar masu gine-gine sun zargi Wike da shiga lamarinsu tare da rushe masu gidaje ba tare da bin doka ba
  • Lauya ya ce, ya kamata shugaban kasa Tinubu ya ja kunnen ministansa na Abuja don dinke barakar da ake fuskanta
  • Tun da aka ba Nyesom Wike minista yake ta rushe-rushe a birnin tarayya, lamarin da ke yiwa mazauna birnin zafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Kungiyar masu gine-gine ta HBAN ta zargi ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike da rushe gidaje sama da 100 ba bisa ka’ida ba a Sabon Lugbe da ke Abuja.

Rushe-rushen Wike, a cewar kungiyar ya raba daruruwan mutane da gidajensu tare da jawo asarar kudaden da basu yi kasa da N200bn ba.

Zargin rushe gidaje da ake yiwa Wike
Ana zargin Wike da rushe gidaje 100 a Abuja | Hoto: Nyesom Wike, HBAN
Asali: UGC

Wike ya ki bin umarnin kotu, inji lauyan HBAN

Kara karanta wannan

Yadda Hadiza Bala Usman ta samu wuka da nama wajen yanka ministocin Tinubu

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, lauyan HBAN Kalu Kalu ya yi ikrarin cewa, Wike na amfani ne da karfin ikonsa na minista wajen aikata wannan rushe-rushe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, masu gidajen na shaida da dukkan takardun da ake bukata wajen mallakar fili da sahhalewar gini a birbin, rahoton Premium Times.

Da yake kira ga shugaban kasa Bola Tinubu ya shiga lamarin, ya ce babu wata kotu da ta ba ma’aikatar Wike ikon rushe gine-ginen kungiyar HBAN.

Tushen matsalar bayan ziyarar Wike

Wannan kitimurmura dai ta soma ne a lokacin da Wike ya kai ziyara yankin a ranar 22 ga watan Oktoba, inda ya alanta mambobin HBAN a matsayin ‘yan mamayar filaye a Abuja.

Kalu ya kuma bayyana cewa, Wike ya yi watsi da duk wani umarni na kotu, inda ya ci gaba da dabbaka aniyarsa ta rushe-rushe baktatan.

Kara karanta wannan

Wike ya bayyana babban aikin da Tinubu ya tura shi ya yi a Abuja

Abuja na daga cikin biranen Najeriya da ke yawan fuskantar rushe-rushen gine-gine daga ministoci da aka taba yi a tarihi, tun lokacin Nasir El-Rufai.

Yadda aka fara rusau a Abuja

A tun farko, hukuma mai kula da cigaban birnin tarayya Abuja (FCDA) ta bayyana aniyar ta na fara yin rusau.

Legit ta gano haka ne cikin wata sanarwa da hukumar ta ba wasu masu shugaba wa'adin sa'o'i 24 domin su tashi.

Rahoton da jaridar Aminiya wallafa ya nuna cewa shagunan da hukumar za ta rushe a karon farko sun kai 500.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.