An Shiga Jimami bayan Jami'in Dan Sanda Ya Harbe Matashi kan N100
- Mutanen ƙaramar hukumar Anambra ta Gabas sun shiga jimami biyon bayan wani aikin aika-aika da jami'in ɗan sanda ya yi
- Jami'in ɗan sandan dai ya harbe wani matashi har lahira bayan rashin jituwa ta ɓarke a tsakaninsu a wani shingen bincike
- Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ƙara da cewa ta fara ɗaukar matakan da suka dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Anambra - Wani jami’in ƴan sanda da ke yankin Otuocha a ƙaramar hukumar Anambra ta Gabas a jihar Anambra ya harbe wani matashi har lahira.
Matashin ya samu rashin jituwa da ƴan sandan ne a wani shingen binciken ababen hawa inda ɗaya daga cikinsu ya ɗauko bindigarsa ya harbe shi.
Wata majiya daga Aguleri a ƙaramar hukumar Anambra ta Gabas ta ce jami'an ƴan sandan da suke a shingen binciken na ƙarƙashin jagorancin wani Onyebuchi ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar, kuma ya dagula al’amura a yankin, yayin da matasa suka nuna rashin amincewarsu da matakin da ƴan sandan suka dauka.
Jaridar The Punch ta ce wata majiya ta bayyana cewa an kashe matashin wanda direban mota ne saboda cin hancin N100.
Ƴan sanda sun yi magana kan lamarin
Hukumomin ƴan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin wanda bai daɗi ba.
Da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya ce sun fara ɗaukar mataki.
"An bayyana sunan ɗan sandan da ya yi harbin a matsayin da Insfeto Sani Suleiman."
"An ƙwace makaminsa kuma an tsare shi domin ci gaba da bincike da kuma bin tsarin ladabtarwa na cikin gida."
- SP Tochukwu Ikenga
Jami'an tsaro sun harbi darakta a Nollywood
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun harbi wani fitaccen daraktan daukar hoto a masana'antar Nollywood.
Jami'an tsaron sun harbi matashin mai suna Don Opata da safiyar ranar Juma'a 1 ga watan Nuwambar 2024 inda yake karbar kulawa a asibiti.
Asali: Legit.ng