Tinubu Ya Fadi Lokacin Kawo Karshen Matsalar Rashin Tsaro a Arewacin Najeriya
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta addabi yankin Arewacin Najeriya
- Shugaba Tinubu ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba matsalar za ta zama tarihi za ta zama tarihi
- Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da su haɗa kai da gwamnati ta hanyar ba da bayanai ga jami'an tsaro domin a magance matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Shugaba Bola Tinubu ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba ayyukan ta’addanci, ƴan bindiga da garkuwa da mutane za su zama tarihi a yankin Arewacin Najeriya.
Shugaba Tinubu ya nanata ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalolin da sauran laifuka a ƙasar nan.
Shugaba Tinubu ya yi wannan alƙawarin ne a Katsina a wajen taron yaye ɗalibai karo na tara na jami’ar tarayya da ke Dutsinma, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya magantu kan rashin tsaro a Arewa
Shugaban ƙasan ya ce magance matsalar rashin tsaro ba aikin gwamnati kaɗai ba ne domin ƴan ƙasa suna da rawar da za su taka ta hanyar ba jami’an tsaro bayanai domin taimakawa yaƙin.
Shugaban ƙasan ya samu wakilcin shugaban jami’ar tarayya dake Dutse a jihar Jigawa, Farfesa Abdulkarim Mohammed.
"Mulki ba wai batun shugaban ƙasa ba ne ko kuma waɗanda ke rike da madafun iko amma batun Najeriya da ƴan Najeriya ne waɗanda za su inganta ƙasar nan."
"Ina so na tabbatarwa ƴan Najeriya cewa gwamnati ta jajirce wajen yaƙar duk wasu ayyukan ta’addanci, garkuwa da mutane, ƴan bindiga da sauran miyagun ayyuka a Najeriya."
"Sai dai, tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa. Ina kira ga ɗaukacin ƴan Najeriya da su haɗa kai da gwamnati ta hanyar ba da bayanan da suka dace ga jami’an tsaro a kan waɗanda ake zargi."
- Bola Tinubu
Batun Tinubu ya fifita Yarbawa a muƙaman tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta yi martani kan iƙirarin cewa gwamnatin Tinubu ta fifita yankin Kudu maso Yamma wajen naɗa shugabannin hukumomin tsaro.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan sadarwa da wayar da kan jama'a, Sunday Dare, ya ce ko kaɗan ba haka abin yake ba.
Asali: Legit.ng