Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani kan Batun Tinubu Ya Fifita Yarbawa a Nadin Shugabannin Tsaro
- Fadar shugaban kasa ta yi magana kan zargin da ake na Shugaba Bola Tinubu ya fi ba da muƙaman shugabannin tsaro ga yankin Kudu maso Yamma
- Mai ba Tinubu shawara kan sadarwa da wayar da kan jama'a, Sunday Dare, ya ce hakan ba gaskiya ba ne
- Sunday Dare ya bayyana kowane yanki na ƙasar nan kujerun da ya samu wajen jagorantar hukumomin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta yi martani kan iƙirarin cewa gwamnatin Tinubu ta fifita yankin Kudu maso Yamma wajen naɗa shugabannin hukumomin tsaro.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan sadarwa da wayar da kan jama'a, Sunday Dare, ya ce ko kaɗan ba haka abin yake ba.
A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X ranar Lahadi, mai taimakawa shugaban ƙasan ya sanya wani teburi da ya ƙunshi shugabannin hukumomin tsaro 20 da kuma yankin da suka fito na ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Naɗin muƙaddasin COAS ya jawo suka ga Tinubu
Rubutun na Sunday Dare ya biyo bayan sukar da aka yi wa Tinubu saboda naɗa Olufemi Oloyede a matsayin muƙaddashin babban hafsan sojoji (COAS).
Ƴan Najeriya da dama a shafukan sada zumunta sun zargi Shugaba Tinubu da fifita yankin Kudu maso Yamma inda nan ne ya fito a naɗe-naɗen nasa.
Olufemi Oloyede zai riƙe muƙamin har sai lokacin da Taoreed Lagbaja ya dawo wanda yanzu haka yake jinya a ƙasar waje.
Wane yafi samun muƙaman tsaro a gwamnatin Tinubu
Sai dai, a teburin da Sunday Dare ya sanya, yankin Arewa maso Yamma ne ke da mafi yawan shugabannin hukumomin tsaro inda yake da kujeru takwas.
Yankin Kudu maso Yamma na da shugabannin hukumomin tsaro biyar yayin da Arewa ta Tsakiya ke matsayi na uku, inda take da muƙamai huɗu.
Shugabannin hukumomin tsaro uku sun fito ne daga yankin Arewa maso Gabas, kamar yadda teburin ya nuna.
Yankunan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas ne ke da mafi ƙarancin adadin mutanen da ke shugabantar hukumomin tsaro a ƙasar nan, inda kowannen su yake da muƙami ɗaya.
Muƙaddashin COAS ya kama aiki
A wani labarin kuma, kun ji cewa muƙaddashin hafsan rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya (COAS), Manjo Janar Olufemi Oluyede ya kama aiki a ofishinsa da ke hedkwatar sojoji a Abuja.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Oluyede ya riƙe mukamin gabanin dawowar hafsan sojojin, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya ɗauki hutun rashin lafiya.
Asali: Legit.ng