Jam'iyyar APC Ta Gayawa Gwamnatin Tinubu Gaskiya kan Tsadar Rayuwa
- Jam'iyyar APC reshen jihar Bauchi ta ba gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu shawara kan halin tsadar rayuwar da ake ciki
- APc ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta ƙara himma wajen rage raɗaɗin da ƴan Najeriya suke a wannan lokacin
- Ta kuma buƙaci gwamnatin da waiwayi aikin haƙo man fetur na Bauchi da Gombe domin amfanin yankin da ƙasa baki ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Jam’iyyar APC a jihar Bauchi, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara himma wajen rage raɗaɗiin da ƴan Najeriya suke ciki.
Jam'iyyar APC ta kuma kira ga ƴan Najeriya da su riƙa yi wa shugabanninsu addu’o’in samun nasarar gudanar da ayyukansu.
An yi wannan kiran ne a cikin sanarwar da aka fitar a ƙarshen taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC reshen jihar da aka gudanar, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban APC na jihar Bauchi, Alhaji Muhammad A. Hassan ne ya sanya hannu a sanarwar bayan taron da aka fitar.
Masu ruwa da tsakin na APC sun kuma nuna goyon bayansu ga manufofin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
APC ta ba Tinubu shawara
Sun kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta dawo da aikin haƙo man fetur na Bauchi da Gombe tare da kammala shi domin amfanin yankin da ƙasa baki daya.
Mahalarta taron dai sun nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ajandarsa ta 'Renewed Hope', da kuma ministocinsa guda biyu daga jihar Bauchi.
Dangane da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan, masu ruwa da tsakin sun bayyana cewa:
"Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta yi wani abu domin rage raɗaɗin da mutane ke sha."
Atiku ya caccaki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi magana kan ƙananan yaran da aka tsare tare da gurfanar da su gaban kuliya kan zanga-zanga.
Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Tinubu kan tsare ƙananan yaran tare da gurfanar da su gaban kuliya saboda zanga-zanga.
Asali: Legit.ng