Gwamna Abba Ya Fadi Matakin Dauka kan Yaran da aka Gurfanar a Kotu

Gwamna Abba Ya Fadi Matakin Dauka kan Yaran da aka Gurfanar a Kotu

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan yaran da aka gurfanar a gaban kotu saboda zanga-zanga
  • Gwamna Abba ya bayyana cewa ya umarci kwamishinan shari'a na jihar ya ɗauki matakin gaggawa kan lamarin
  • Gwamnan ya ba da tabbbacin cewa za su.yi duk mai yiwuwa domin ganin yaran sun dawo zuwa Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki dukkan matakan da suka dace domin dawo da ƙananan yara da ake kyautata zaton wasu ƴan Kano ne.

A ranar Juma’a ne aka gurfanar da mutane da dama da suka hada da ƙananan yara a gaban kuliya bisa zarginsu da hannu a zanga-zangar #EndBadGovernance.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya soki gurfanar da kananan yara kotu, ya ba gwamnati shawara

Gwamna Abba ya yi magana kan kai yara kotu
Gwamna Abba ya ce za su yi kokarin dawo da yaran da aka kai kotu zuwa Kano Hoto: @Kyusufabba, @YeleSowore
Asali: Twitter

Gwamna Abba ya magantu kan kai yara kotu

Da yake mayar da martani kan lamarin a shafinsa na X, Gwamna Abba ya ce, ya umarci kwamishinan shari'a na jihar, Haruna Dederi, ya ɗauki matakin gaggawa kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya bayyana hakan ne bayan ya samu labarin halin da yaran suke ci.

"An ja hankalina kan bayyanar yara (wasu da ake kyautata zaton ƴan Kano ne) a kotu a birnin tarayya Abuja."
“An umarci kwamishinan shari’a da ya gaggauta ɗaukar mataki kan lamarin. Za mu yi duk abin da ya dace domin dawo da su zuwa Kano Insha Allah."

- Abba Kabir Yusuf

An gurfanar da yara a kotu

Waɗanda aka kama sun fito ne daga Abuja, Kaduna, Gombe, Jos, Katsina, da kuma Kano. Laifukan da ake tuhumar su da su sun haɗa da ta’addanci, ƙone-ƙone, da kuma laifin cin amanar ƙasa.

Kara karanta wannan

Jami'an EFCC sun kama Akanta Janar da wasu hadiman gwamna 4, bayanai sun fito

An gurfanar da masu zanga-zangar ne a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja inda wasu ƙananan yara huɗu suka sume, sannan aka fitar da su yayin da ake ci gaba da shari’a.

IGP ya faɗi dalilin yara na sumewa a kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa sufeto-janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya yi magana kan sumar da wasu daga cikin yaran da gurfanar a gaban kotu suka yi.

Shugaban ƴan sandan ya bayyana cewa sumar da shida daga cikin yaran suka yi, kafin a gurfanar da su a gaban kuliya, wani shiri ne da aka shirya domin jawo hankulan mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng