Zanga Zanga: Lauyan Gwamnatin Tinubu Ya Fayyace Dalilin Maka ‘Kananan’ Yara a Kotu

Zanga Zanga: Lauyan Gwamnatin Tinubu Ya Fayyace Dalilin Maka ‘Kananan’ Yara a Kotu

  • Gwamnatin tarayya ta bakin lauyanta, ta bayyana hikimar gurfanar da wadanda aka cafke a wajen zanga-zanga
  • Lauyan da ya tsayawa gwamnati, Rimazonte Ezekiel ya tabbatar da cewa yaran da aka kai kotu sun kai shekara 18
  • Barista Rimazonte Ezekiel ya zargi wadanda ake tuhuma da neman kifar mulkin farar hulda da ake cin moriyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi magana a sakamakon gurfanar da wasu yara da aka yi a kotu bisa zargin neman kifar da gwamnati.

Lauyan da ya tsayawa gwamnatin Najeriya wajen shigar da karar ya musanya zargin da ake yi masu na yin shari’a da kananan yara.

Yara.
Yaran da aka kama wajen zanga zanga a kotu Hoto: Adeyanju Deji
Asali: Facebook

Lauyan gwamnati ya kare kama 'yan zanga-zanga

Kara karanta wannan

Muguntar T pain: Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu kan kai yara kotu

Rimazonte Ezekiel ya zanta da manema labarai bayan an yi zama a kotun tarayya, tashar Channels ta rahoto maganar da aka yi da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barista Rimazonte Ezekiel ya karyata zancen da yake yawo a gari, ya hakikance cewa duka wadanda aka kai kotu sun kai shekara 18.

Zanga-zanga: 'Ba kananan yara ba ne' - Lauya

Lauyan yake cewa a cikin yara fiye da 67 da ake shari’a da su akwai wadanda sun yi aure.

Kamar yadda lauyan da ya shigar da kara a madadin gwamnatin Bola Tinubu ya fada, wasu cikin wadanda ake tuhuma sun gama jami’a.

An ji Rimazonte Ezekiel ya na cewa a yi watsi da ikirarin da ake yi cewa an shiga hakkin yaran, ya zarge su da neman kifar da gwamnati.

Bayan shekara da shekaru ana kokarin kawo mulkin farar hula, lauyan ya ce wadanda ake tuhuma sun nemi sojoji su yi juyin mulki.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Amnesty ta bukaci Tinubu ya gaggauta sakin yaran da aka kai kotu

A cewar Ezeikiel, lauyoyin da suke kare masu zanga-zangar ba su san asalin yaran ba. Dazu The Cable ta tabbatar da wannan a rahotonta.

Abin da Lauya ya fadawa jama'a

"Wadannan yaran da mu ka kawo kotu duka baligai ne. mafi yawancinsu masu aure ne, a cikinsu babu mai karancin shekaru.
"Masu tsaya masu sun san wadanda su ke karewa a kotu?

- Lauyan gwamnati

Gwamnati ta zarge su da daga tutocin kasashen ketare kamar Rasha a lokacin da aka yi wa gwamnatin Bola Tinubu zanga-zanga a Agusta.

Atiku ya soki tsare masu zanga-zanga

Dazu rahoto ya zo cewa Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da kai ƙananan yara gaban kotu da sunan za su kifar da gwamnatin Bola Tinubu.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya caccaki gwamnatin Tinubu kan ɗaukar matakin da ya ce ya akwai rashin tausayi a aikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng