Gwamna Ya Yi Alkawarin Fara Biyan Sabon Mafi Karancin Albashin N73,000 a Watan Zaɓe

Gwamna Ya Yi Alkawarin Fara Biyan Sabon Mafi Karancin Albashin N73,000 a Watan Zaɓe

  • Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ce gwamnatinsa za ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N73,000 a watan Nuwamba, 2024
  • A ranar 21 ga watan Nuwamban da muke ciki za a gudanar da zaɓen gwamna a jihar Ondo da Aiyedatiwa ke takara a inuwar APC
  • Gwamnan ya tabbatarwa ma'aikata cewa idan har Allah ya ba shi nasara a zaɓen da za a yi, zai nunka ayyukan da ya yi a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo - Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya ce za a fara biyan sabon mafi karancin albashi na ₦73,000 ga ma’aikatan gwamnati daga watan Nuwamba.

Idan ba ku manta ba, hukumar zaɓe INEC ta tsara gudanar da zaɓen gwamnan jihar Ondo a watan Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

Shugaban malamai ya dauki alkawarin tallata ɗan takarar APC

Lucky Aiyedatiwa.
Gwamnan Ondo yayi alkawarin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi a watan zabe Hoto: Hon. Lucky Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Gwamna Aiyedatiwa ya ce walwala da jin daɗin ma'aikata na ɗaya daga cikin abubuwan da gwamnatinsa za ta fi ba fifiko, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi ga ma'aikatan jihar Ondo bayan wani tattakin motsa jiki a Akure.

Gwamna Aiyedatiwa zai ba ma'aikata fifiko

Mai girma gwamna ya ce:

"Duk wani abu da muka yi wa ma’aikata ba siyasa ba ce, idan ma'aikata ba su yi farin ciki ba, ba za a ƙarfafa su ba. Hakan ya sa a koda yaushe muke ba da fifiko ga walwalarsu.”

Gwamna Aiyedatiwa ya jaddada muhimmancin bai wa ma'aikata ƙwarin guiwa domin a cewarsa ta haka ne za su sauke nauyin da ke kansu cikin jin daɗi.

Gwamnan Ondo ya ɗauki alkawari

Lucky Aiyedatiwa ya tabbatarwa ma'aikatan cewa idan har ya samu nasara a zaben da za a yi, zai nunka nasarorin da ya samu a yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gabatar da N40,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi? TUC ta yi bayani

Ya kuma nuna jin daɗi bisa yadda ma'aikata suka ba shi haɗin kai, sannan ya tuna masu matsayinsa na ma'aikaci lamba ɗaya a jihar Ondo, Punch ta rahoto.

Gwamna ya yi kamu ana dab da zaɓe

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya karbi wata kusa a jam'iyyar SDP ana daf da gudanar da zaɓe.

Gwamnan ya karbi mataimakiyar dan takarar gwamna a jam'iyyar SDP, Susan Gbemisola Alabi ana shirin zaɓe a jihar Ondo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262