EFCC Ta Cafke Bobrisky Zai Sulale London, Ya Bukaci Taimako
- Hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta cafke shahararren dan daudu da aka fi sani da Bobrisky
- Rahotanni na nuni da cewa an kama dan daudun ne yayin da ya shiga jirgi domin tafiya kasar Birtaniya a filin jirgin sama a Legas
- Hukumar EFCC ta bayyana cewa akwai sababbin laifuffukan da ta ke zargin Bobrisky a kansu kuma haka ne dalilin kama shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Jami'an hukumar EFCC sun tabbatar da sake kama fitaccen dan daudu, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky.
Wannan shi ne karo na biyu da aka cafke Bobrisky yana shirin ficewa daga Najeriya tun bayan fitowarsa daga gidan kurkuku.
Jaridar Punch ta wallafa cewa EFCC ta ce za ta taho da Idris Okuneye zuwa Abuja domin cigaba da bincikensa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar EFCC ta kama Bobrisky a Legas
Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa ta cafke shahararren dan daudu, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky.
Jami'in hulda da jama'a na EFCC, Wilson Uwajaren ne ya bayyana haka yayin da yake bayani ga manema labarai.
Daily Post ta wallafa cewa shi ma dan daudun ya tabbatar da cewa EFCC sun kama shi yana shirin tafiya London a cikin wani jirgi.
Ga abin da yake cewa:
"Ya ku yan Najeriya! Ku taimaka mini. Jami'an EFCC sun kama ni, kuma na ji rauni sosai"
- Bobrisky
Dalilin kama Bobrisky a Legas
Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta cafke Bobrisky ne saboda ya zarge ta da karɓar cin hanci da rashawa.
Bayan zargin, hukumar ta ce ta gayyaci dan daudun domin amsa tambayoyi amma ya yi kunnen uwar shegu.
A yanzu haka dai za a tafi da shi hedikwatar EFCC da ke birnin tarayya Abuja domin amsa tambayoyi.
Bobrisky ya koka kan rashin lafiya
A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen dan daudun nan, Idris Okuneye ya kwana a wani asibiti da ke jihar Lagos saboda rashin lafiya ta gaggawa.
Yayin da aka je ofishin yan sanda, dan daudun da aka fi sani da Bobrisky ya yi korafi kan wani irin ciwo da yake ji a cikin nonuwansa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng