Zanga Zanga: Kananan Yaran da Aka Kama Sun Sume a Gaban Alkali, An Gano Dalili

Zanga Zanga: Kananan Yaran da Aka Kama Sun Sume a Gaban Alkali, An Gano Dalili

  • An shiga tashin hankali da wasu daga cikin ƙananan yaran da ake zargi suka suma a gaban alkalin babbar kotun tarayya mai zama a Abuja
  • Yaran wadanda aka kama su a Kano lokacin zanga-zanga sun yanki jiki sun faɗi a lokacin da ƴan sanda suka gurfanar da su a kotu
  • Lauyan waɗanda ake tuhuma ya ce wannan alama ce da ke nuna ba su samun abinci da kulawar da ta dace a hannun ƴan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wasu daga cikin ƙanann yaran da ƴan sanda suka cafke lokacin zanga-zangar yunwa sun sume a gaban Alkalin babbar kotun tarayya mai zama a Abuja

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya afku ne a lokacin da ƴan sanda suka kawo waɗanda ake tuhumar gaban Mai Shari'a Obiora Egwuatu.

Kara karanta wannan

Kaico: Wani matashin yaro ɗan shekara 16 ya hallaka kishiyar mahaifiyarsa

Babbar kotun tarayya.
Yaran da aka kama lokacin zanga-zanga sun suma a gaban alkali Hoto: Federal High Court
Asali: Getty Images

Channels tv ta ce yaran da jami'an tsaron suka kama su 75 ba su wuce shekara 12 zuwa 15 ba, kuma ana zarginsu da ta'addanci da yunkurin kifar da gwamnati da sunan zanga-zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama kananan yara a Kano

Jami'an tsaro sun kama su ne ranar 3 ga watan Agusta, 2024 kuma tun wannan lokaci suna tsare a hannun ƴan sanda.

Ana zargin dai suna daga cikin waɗanda suka shiga zanga-zangar yunwa, inda suka rika rera waƙoƙin adawa da gwamnati da ɗaga tutar Rasha a jihar Kano.

Ɗaya daga cikin lauyoyin waɗanda ake kara, Marshall Abubakar ya ce an gurfanar da yaran ƙashi biyu, kashi na farko su 76 da kashi na biyu su 49.

Kananan yaran da ake tuhuma sun suma a kotu

Bayan an kira na farko, sun taso da nufin zuwa wurin da aka warewa waɗanda ake tuhuma, kwastam wasu daga cikinsu akalla yara biyar suka faɗi ƙasa sumammu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutane masu yawa a mahaifar tsohon gwamna

Lamarin dai ya haifar da ruɗani da tashin hankali a kotun, wanda ya sa alkali ya sanar da ɗage zaman nan take.

Tuni dai aka kira malaman lafiya na asibitin kotun domin su duba waɗanda suka yanke jiki suka faɗi, kamar yadda The Nation ta kawo.

Wane halin yaran ke ciki?

Lauyan yaran, Marshall Abubakar ya ce abin da ya faru alama ce ta yunwa da rashin lafiya, inda ya ce kusan dukkannsu yara ne da ba su wuce shekara 12 ba.

"Yaran nan ba su da lafiya, ga yunwa. An ajiye su a hannun 'yan sanda na tsawon makonni ba tare da abinci da kulawar da ta dace ba. Ba su da lafiya kuma suna buƙatar kulawa," in ji shi.

An yi zanga-zangar tunawa da ENDSARS

A wani rahoton, kun ji cewa masu zanga-zanga sun mamaye Lekki Toll Gate da ke Legas domin tunawa da ranar da aka yi zanga-zangar EndSARS karo na 4.

An ce sun yi taron ne domin sake nuna takaicin su kan zaluncin ‘yan sanda da kuma kashe matasan da aka yi shekaru hudu baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262