EFCC Ta Bi Tsofaffin Gwamnoni, Ta Koma kan Manyan Jami'an Bankuna a Najeriya

EFCC Ta Bi Tsofaffin Gwamnoni, Ta Koma kan Manyan Jami'an Bankuna a Najeriya

  • Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta ce ta yi nasarar ɗaure ma'aikatan bankuna bisa almundahana
  • Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya ce sun samu nasarori a yaƙin da su ke yi da cutar da tattalin arziƙin Najeriya a cikin shekara
  • Olukoyede ya bayyana cewa jami'an EFCC za su cigaba da aiki tuƙuru domin daƙile ayyukan da za su yi wa tattalin arziki illa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta ce ba za ta saurarawa manyan jami'an bankuna da ake zargi da hannu a almundahana ba.

Kara karanta wannan

Banki a Najeriya ya ƙara cajin hada hadar kudi, ya fitar da bayanai

Hukumar ta ƙara da cewa yanzu haka akwai manyan ma'aikatan bankuna da ta ke fako bisa zarge-zargen almundahana.

Hukuma
EFCC ta na binciken manyan ma'aikatan banki Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa akwai ma'aikatan da ake tuhumarsu da laifuffuka daban-daban a kotunan ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar EFCC na binciken ma'aikatan bankuna

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa hukumar EFCC ta fara binciken manyan ma'aikatan wasu bankuna da ake zargi da ba da haɗin kai domin almundahana.

Shugaban EFCC na ƙasa, Ola Olukoyede ya bayyana cewa duk wadanda kotu ta tabbatarwa da laifin da ake zarginsa da shi zai yi zaman gidan kaso.

EFCC: Kotu ta ɗaure wasu ma'aikatan bankuna

Da ya ke jawabi a madadin shugaban EFCC, kakakin hukumar, Wilson Uwajaren ya ce sun yi nasara wajen ɗaure manyan ma'aikatan bankuna biyar.

A ƙarin bayani kan nasarorin da EFCC ta samu a cikin shekara daya, ya ce ba za su saurarawa duk masu jawo matsala ga tattalin arziƙi ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi rawar da bangaren shari'a zai taka wajen magance rashin tsaro

Jigawa ta daina neman a rusa EFCC

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta janye daga ƙarar da ke neman kotu ta tilasta ruguza hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati.

Kwamishinan Shari'a na jihar, Bello AbdulKadir Fanini ne ya faɗi matsayar gwamnatin Jigawa, ya ce an shigar da janye ƙarar a ranar 24 Oktoba, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.