"Akwai Yunwa a Kasa" Gwamnoni Sun Tausayawa Ƴan Najeriya, Sun Hango Sauƙi
- Gwamnonin jihohi 36 sun tabbatar da cewa ƴan Najeriya na fama da yunwa sakamakon manufofin da shugaban ƙasa ya zo da su
- Sai dai duk da haka gwamnonin sun bayyana cewa suna fatan nan ba da daɗewa ba mutane za su samu sauƙi su amfana da tsare-tsaren
- Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce gwamnoni na tausayawa ƴan Najeriya saboda halin da suka tsinci kansu a mulkin nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnonin jihohi 36 sun aminta da cewa ƴan Najeriya na fama da yunwa amma suna ganin za a samu sauƙi nan gaba.
Gwamnonin sun bayyana haka ne bayan taron kungiyar gwamnonin Najeriya watau NGF wanda ya gudanar ranar Laraba da daddare.
Gwamnonin sun ce suna sane da cewa ‘yan Najeriya na fama da yunwa amma sun nuna kwarin guiwa kan tsare-tsaren Bola Tinubu, Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnoni sun gayyaci shugaban NNPCL
Kalaman gwamnonin na zuwa ne bayan shugaban kamfanin mai na ƙasa NNPCL, Mele Kyari ya yi masu bayani a taron da suka yi a Abuja.
Mele Kyari ya tabbatarwa gwamnonin cewa a halin yanzu an cire tallafin man fetur gaba ɗaya, babu sauran abin da ya rage.
Ya kuma shaidawa gwamnonin kalubalen da kamfanin NNPCL ke fuskanta da kuma shirin da yake yi na rage raɗaɗin ƙarin farashin litar fetur da ake yi a kai-a kai.
Idan dai ba ku manta ba an kara farashin man fetur sau uku a cikin kwanaki 60, lamarin da ya kara jefa jama’a cikin ƙarin wahala da ƙuncin rayuwa.
Gwamnoni sun ce za a samu sauƙi
Da yake hira da manema labarai a madadin gwamnoni bayan taron, Gwamna Hope Uzodinma na Imo ya ce suna fatan za a samu sauƙi nan bada daɗewa ba.
A rahoton Leadership, gwamnan ya ce:
"Fatanmu abubuwa su yi kyau a kowane lokaci daga yanzu, muna tausayawa mutane, mun san suna shan wahala sosai a ƙasar nan.
"Muna tare da manufofin shugaban ƙasa, addu'armu kawai Allah ya kawo sauƙi da wuri-wuri ta yadda ƴan Najeriya za su fara amfana da tsare-tsaren Tinubu."
Gwamnatin Tinubu ya tallafawa mutane
A wani labarin, an ji cewa Gwamnatin tarayya ta ce zuwa yanzu ta turawa ƴan Najeriya miliyan 25 har N25,000 domin rage raɗaɗin halin da ake ciki.
Ministan kudi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan taron majalisar tattalin arziƙi NEC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng