Gini Ya Rufto kan Mutane, Mutum 10 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya
- An samu ruftowar gini a birnin Ibadan na jihar Oyo da safiyar ranar Alhamis, 31 ga watan Oktoban 2024
- Ruftowar ginin ta yi sanadiyyar rasuwar mutane 10 yayin da wasu mutum bakwai suka samu raunuka daban-daban
- Hukumar kashe gobara ta jihar Oyo wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta ce jami'anta na ci gaba da aikin ceto
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Oyo - Aƙalla mutane 10 ne suka mutu sakamakon ruftawar wani gini a jihar Oyo.
Wasu mutane bakwai kuma sun samu raunuka sakamakon ruftawar ginin a Ibadan, babban birnin jihar Oyo da safiyar ranar Alhamis.
Wata sanarwa da hukumar kashe gobara ta jihar Oyo ta fitar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a unguwar Jegeda Oluloyo da ke Ibadan a ƙaramar hukumar Ona Ara, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gini ya ruftowa mutane a Ibadan
Sanarwar ta ƙara da cewa, yayin da aka kwaso gawar mutane 10 daga cikin ɓuraguzan ginin, an kuma ceto mutane bakwai da ransu, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
"Hukumar kashe gobara ta jihar Oyo ta samu kiran waya da safiyar yau a unguwar Jegede Olunloyo da ke Ibadan kan ruftawar wani gini."
"An ciro gawar mutane 10 daga cikin ɓuraguzan ginin da ya ruguje, yayin da aka ceto mutane bakwai da ransu. Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto."
Jaridar Leadership ta rahoto cewa shugaban hukumar kashe gobara ta jihar, Yemi Akinyinka, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
"Lokacin da muka isa wurin, mutane 10 sun mutu. An ceto mutum uku kafin mu isa wurin, kuma mutanen mu sun samu nasarar ceto mutane huɗu. Har yanzu suna ci gaba da aikin ceto."
- Yemi Akinyinka
Gini ya rufto kan mutane a Abuja
A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutane 40 ne ake fargabar sun maƙale bayan ruftawar wani gini a ranar Asabar a unguwar Sabon Lugbe da ke babban birnin tarayya Abuja.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa aƙalla mutane 40 ne suka maƙale a ginin wanda ya rufto a ranar Asabar, 27 ga watan Oktoban 2024.
Asali: Legit.ng