Gwamna APC Ya ba da Hutun Kwanaki 2, Ya Bayyana Dalili

Gwamna APC Ya ba da Hutun Kwanaki 2, Ya Bayyana Dalili

  • Gwamnan jihar Cross Rivers, Bassey Otu ya ba da hutun kwanaki biyu domin zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi a jihar
  • Ottu ya ayyana ranakun Alhamis da Juma'a a matsayin ranakun da babu aiki domin zaɓen na ranar Asabar, 2 ga watan Nuwamban 2024
  • Gwamnan ya ba da hutun ne domin ne ba da dama ga mutanen da ke nesa su yi tafiya zuwa yankunan da suke kaɗa ƙuri'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Cross Rivers - Gwamnan jihar Cross Rivers, Bassey Otu, ya ayyana ranakun Alhamis da Juma’a a matsayin ranakun hutu.

Gwamna Bassey Otu ya ba da hutun ne domin zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a gudanar.

Gwamnan Cross Rivers ya ba da hutun kwanaki biyu
Gwamna Bassey Otu ya ba da hutun kwanaki biyu domin zaben ciyamomi Hoto: @Officialspbo
Asali: Twitter

Gwamna Otu ya ba da hutu domin zaɓen ciyamomi

Kara karanta wannan

Gwamna ya maida martani, ya ce har yanzu ƴan Arewa na tare da Shugaba Tinubu

Babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Nsa Gill, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa hutun zai ba mutane damar yin tafiya zuwa yankunan da suke kaɗa ƙuri'a, rahoton PM News ya tabbatar.

Za a gudanar da zaɓen ne a ranar 2 ga watan Nuwamba a faɗin ƙananan hukumomi 18 na jihar.

Gwamna ya yi kira ga jama'an Cross Rivers

Ya buƙaci jama'a da su yi amfani da hutun tare da shiga harkokin zaɓe domin su zaɓi ƴan takarar da suke so.

"A yunƙurin tabbatar da cewa mutanen Cross Rivers sun shiga zaɓen ciyamomi na ranar 2 ga watan Nuwamba, Gwamna Bassey Otu ya ayyana ranakun Alhamis, 31 ga Oktoba da Juma'a, 1 ga Nuwamba a matsayin ranakun hutu a jihar."
"Gwamna Otu ya ce an ɗauki matakin ne domin ba da isashshen lokaci ga waɗanda za su yi tafiya daga Calabar zuwa yankunan da ke lungu domin yin amfani da damarsu ta kaɗa ƙuri'a a zaɓen."

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi rawar da bangaren shari'a zai taka wajen magance rashin tsaro

- Nsa Gill

Ƴan APC sun koma PDP a Cross Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Cross Rivers ta samu koma baya da wasu manyan jagororinta sun koma jam'iyyar PDP.

Kimanin jagorori 500 na jam’iyyar APC a ƙananan hukumomi bakwai na mazaɓar Sanatan Cross Rivers ta Kudu suka tsallaka zuwa jam'iyyar PDP mai adawa a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng