Gwamnonin Jihohi Sun Gana a Abuja kan Muhamman Batutuwa 4, Bayanai Sun Fito

Gwamnonin Jihohi Sun Gana a Abuja kan Muhamman Batutuwa 4, Bayanai Sun Fito

  • Kungiyar gwamnonin jihohin Najeriya ta yi zama a Abuja domin duba muhimman batutuwa da suka shafi ƙasa
  • Gwamnoni 36 sun tattauna kan batun ƴancin ƙananan hukumomi, wadatar abinci, tsaro da rikici a ɓangaren mai
  • Bayanai sun nuna gwamnonin sun fara wannan zama da misalin karfe 9:30 na daren jiya Laraba a sakatariyar NGF

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnonin jihohin ƙasar nan 36 sun gana a sakateriyar ƙungiyar gwamnoni NGF da ke babban birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun nuna gwamnoni sun yi zama ne domin tattaunasa batutuwan da suka shafi ƙasa kamar ƙarancin abinci da rikicin da ya ɓarke a ɓangaren mai.

Gwamnonin jihohi.
Gwamnoni 36 a Najeriya sun gana a Abuja Kan Muhimman batutuwa Hoto: Nigeria Governors Forum
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa taron ya gudana ne karkashin jagorancin shugaban NGF kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman Abdulrazaq.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi rawar da bangaren shari'a zai taka wajen magance rashin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sun nuna cewa gwamnonin sun shiga wannan taro ne da misalin ƙarfe 9:30 na daren jiya Laraba, 29 ga watan Oktoba, 2024.

Abubuwan da gwamnonin suka tattauna

Daga cikin abubuwan da taron ya kunsa, shugaban kamfanin mai na ƙasa NNPCL, Mele Kyari zai yi wa gwamnonin bayani kan abubuwan da ke faruwa a ɓangaren mai.

A rahoton Channels tv, gwamnonin sun kuma tattauna batutuwan da suka shafi shari’o'in da kungiyarsu ke fuskanta ciki har da batun ƴancin kananan hukumomi.

Haka zalika akwai yiwuwar gwamnonin za su saurari bayani kan sha'anin tsaro daga wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkokin tsaron ƙasar nan.

Gwamnoni sun damu da batun tsaron ƙasa

Daga cikin waɗanda za su halarci zaman gwamnonin don yi masu bayani kan lamarin tsaro har da shugaban hukumar tsaron farin kaya (DSS), Adeola Oluwatosin Ajayi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga ganawa da Aliko Dangote, an samu bayanai

Sai kuma.ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, wanda Lami Chinade zai wakilta.

Bugu da ƙari, gwamnonin za su duba yiwuwar ware Dala miliyan 825 domin inganta fannin noma a Najeriya.

Gwamnoni, Sarakuna sun gana da Tinubi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Najeriya da sarakunan gargajiya suna ganawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa.

Ana hasashen cewa shugabannin suna ganawa ne domin neman mafita ga yan Najeriya kan halin da ake ciki a yau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262