Kaduna: Likitar da Aka Sace Ta Dawo Gida bayan Watanni 10 a Hannun Ƴan Bindiga
- Bayan shafe kusan watanni 10 a hannun ƴan bindiga, Dr. Ganiyat Popoola da ke aiki a asibitin ido na Kaduna ta shaƙi iskar ƴanci
- Shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa watau NARD, Tope Zenith Osundara ya tabbatar da sako likitar ranar Laraba
- Ranar 27 ga watan Disamba, 2023 aka yi garkuwa da likitar tare da mijinta da wani ɗan uwanta da ke zaune tare da su a Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Kwararriyar likitar nan a Kaduna, Dr Ganiyat Popoola ta shaƙi iskar ƴanci watanni 10 bayan ƴan bindiga sun yi garkuwa da ita.
An yi garkuwa da Dokta Popoola, magatakarda a sashin kula da ido a asibititn ido na kasa da ke Kaduna, a ranar 27 ga Disamba, 2023.
Kaduna: Yadda aka sace likitar da mijinta
Ƴan bindiga sun sace Likitar tare da mijinta, Nurudeen Popoola, da kuma dan uwanta, Folaranmi Abdul-Mugniy, wanda ke zaune tare da su, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan diguwar tattaunawa masu garkuwa da mutanen, an sako mijin a ranar 8 ga Maris, 2024, amma ƴan bindigar sun ci gaba da rike likitar da Abdul-Mugniy.
Kungiyar likitoci masu neman kwarewa NARD ta sha fitowa zanga-zanga a fadin kasar nan, tana mai kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta ceto likitar.
NARD ta tabbatar da sakin likita
Amma a yau Laraba da yamma, masu garkuwa sun sako likitar tare da ɗan uwanta bayan su shafe kusan shekara guda a tsare.
Shugaban NARD, Tope Zenith Osundara, ya tabbatar da hakan a wata hira da wakilin jaridar ta wayar tarho, rahoton Punch.
"Eh gaskiya ne, an sako ta yau Laraba, a halin yanzu mun killace ta daga mutane, ba mu son a dame ta, mutane kaɗan muke bari su gnata."
Da aka tambaye shi ko nawa aka biya domin a sako ta, sai ya amsa da cewa “Ba a biya ko kwabo da sunan kudin fansa ba.”
Ƴan bindiga sun nemi kuɗin fansar limamin coci
A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga sun nemi a lale masu Naira miliyan 200 a matsayin kudin fansar limamn cocin katolika da suka sace a Edo.
A ranar Lahadi ne masu garkuwa suka yi awon gaba da Rabaran Thomas bayan sun yi yunkurin sace wasu ɗalibai biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng