Majalisa Ta Dauki Mataki kan Bukatar Tinubu Ta Amincewa da Nadin Ministoci

Majalisa Ta Dauki Mataki kan Bukatar Tinubu Ta Amincewa da Nadin Ministoci

  • Majalisar dattawa ta amince da sababbin ministoci bakwai da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa
  • Majalisar ta amince da su ne bayan ta tantance su yayin zamanta na ranar Laraba, 30 ga watan Oktoban 2024
  • Shugaban majalisar dattawa ya nuna gamsuwarsa kan mutanen da Tinubu ya zaɓo domin su zama ministoci a gwamnatinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta amince da sababbin ministoci bakwai da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa kwanan nan a gwamnatinsa.

Majiyar dattawan ta amince da ministocin ne bayan ta tantance su a ranar Laraba.

Majalisa ta amince da nadin ministoci
Majalisar dattawa ta amince da sababbin ministocin da Tinubu ya nada Hoto: Dr. Jumoke Oduwole, Dr. Nentawe Goshwe Yilwatda, Bianca Odumegwu-Ojukwu
Asali: Facebook

Majalisa ta tantance ministocin Tinubu

Jaridar The Cable ta rahoto cewa majalisar ta amince da sababbin ministocin ne yayin zaman majalisar na ranar Laraba, 30 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara tantance sababbin ministocin Tinubu, an samu bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Laraba ne dai majalisar dattawan ta fara tantance ministocin guda bakwai waɗanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa.

Ministocin sun haɗa da Jumoke Oduwole ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Idi Muktar Maiha, ministan kiwon dabbobi, Yusuf Ata, ƙaramin ministan gidaje da raya birane, da Suwaiba Said Ahmad, ƙaramar ministar ilimi.

Sauran sun haɗa da Nentawe Goshwe Yilwatda ministan jin ƙai da rage talauci, Muhammadu Dingyadi a matsayin ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Bianca Ojukwu a matsayin ƙaramar ministar harkokin ƙasashen waje.

A lokacin tantance su, ministocin sun yi magana kan yadda za su yi amfani da ofisoshinsu ta yadda ƴan Najeriya za su amfana.

Ministocin Tinubu sun samu amincewar majalisa

An amince da ministocin ne bayan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya buƙaci a kaɗa ƙuri'a.

Akpabio ya bayyana cewa ya gamsu da zaɓen da Shugaba Tinubu ya yi na ministocin.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga ganawa da Aliko Dangote, an samu bayanai

"Ina tunanin shugaban ƙasa ya ɗauki lokacinsa wajen zaɓo waɗannan ministocin."

- Godswill Akpabio

Majalisar dattawa ta waiwayi ministocin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta fara shirye-shiryen tantance sababbin ministocin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin majalisar dattawa, Basheer Lado, ya tabbatar da cewa sababbin ministocin sun fara bin matakan doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng