Gwamna Ya Maida Martani, Ya Ce Har Yanzu Ƴan Arewa na Tare da Shugaba Tinubu
- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya musanta raɗe-raɗin da ake cewa ƴan Arewa sun dawo daga rakiyar Bola Tinubu
- Sule ya bayyana cewa ba zai yiwu Arewa ta tsaya kai da fata har shugaban ƙasa ya samu nasara kuma ta dawo tana faɗa da shi ba
- Gwamnan ya ce shi da takwarorinsa ba su yarda da sabon tsarin harajin da aka ɓullo da shi ba saboda ba a yi wa Arewa adalci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Nasarawa - Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule ya musanta rade-radin da ake cewa yankin Arewacin kasar na adawa da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Gwamma Sule ya ce har yanzun ƴan Arewa na goyon bayan shugaba Tinubu saɓanin jita-jitar da ake yaɗawa.
Abdullahi Sule ya bayyana haka ne a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnoni a Arewa sun koka kan haraji
Hakan na zuwa ne bayan kungiyar gwamnonin Arewa ta yi fatali da sabon tsarin harajin VAT da ake shirin ɓullo da shi.
A taron da suka yi ranar Litinin, gwamnonin Arewa sun yi watsi da kudirin haraji wanda yanzu haka ya isa gaban majalisar tarayya.
Tun daga nan aka fara yaɗa jita-jitar cewa Arewa ta dawo daga rakiyar shugaba Bola Tinubu.
Gwamna ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa
Amma Gwamna Sule ya ce duba da goyon bayan xa yankin ya ba Tinubu a zaɓen 2023, babu dalilin da zai sa ƴan Arewa su ƙullaci shugaban ƙasa.
"Ba zai yiwu mu kawo Tinubu kuma ƴan Arewa su tsaya kai da fata har ya zama shugaban ƙasa kuma daga baya mu juya masa baya ba," in ji Sule.
Gwamna Abdullahi Sule ya ƙara da cewa gwamnonin Arewa sun yi fatali da sabon tsarin harajin ne saboda ba a yi wa yankinsu adalci ba.
Gwamna Sule ya kare Bola Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya kare Bola Ahmed Tinubu kan tsadar rayuwar da ake fama da ita.
Gwamna Sule ya bayyana cewa shugaban Najeriya Tinubu yana sane da halin ƙuncin da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a gwamnatinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng