Sai bayan Mako 2: An Kara Shiga Ruɗani kan Gyaran Wutar Arewa
- Gwamnatin tarayya ta kara bayani kan lokacin da wutar lantarki za ta kammala dawowa a jihohin Arewacin Najeriya
- Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya tabbatar da sai ranar 12 ga watan Nuwamba za a kammala gyaran wutar Arewa
- Hakan na zuwa ne bayan an shafe kwanaki 10 babu lantarki a jihohi 17 a yankin Arewacin Najeriya saboda lalacewar layin wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya yi bayani kan samun cikakken gyaran wutar lantarki a Arewacin Najeriya.
Adebayo Adelabu ya ce shawo kan matsalar dari bisa dari zai dauki kimanin mako biyu masu zuwa.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Adebayo Adelabu ya yi bayani ne ga Sanatocin Najeriya a kan matsalar lantarkin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a yi mako 2 kafin gyara wutar Arewa
Ministan makamashi, ya tabbatar da cewa kafin a kammala gyaran wutar lantarki a Arewacin Najeriya dari bisa dari, za a dauki mako biyu, zuwa 12 ga Nuwamba.
Adebayo Adelabu ya bayyana haka ne a gaban majalisar dattawan Najeriya yayin da yake bayani kan halin da ake ciki.
"Ina mai tabbatar muku cewa nan da kwanaki 14 za a kammala gyaran wutar kuma za a samu cikakkiyar wutar lantarki.
Muna aiki da jami'an tsaro domin samun isa wajen gyaran wanda a yanzu haka yan bindiga ke kewaye da shi."
-Adebayo Adelabu, ministan makamashi
Maganar gyaran wuta ta wucin gadi
Sai dai ministan ya kara da cewa za a yi gyaran wucin gadi a tsawon kwanaki uku zuwa biyar domin fara samun wutar.
Business Day ta wallafa cewa a yanzu haka jihohin Kwara da Neja ne kawai ke samun wutar lantarki a yankin Arewacin Najeriya.
Hakan na nuni da cewa dukkan sauran jihohi 17 na Arewacin Najeriya na fama da matsalar wutar lantarki.
Gwamnati za ta kafa wutar sola a Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fara shirin samar da wuta mai amfani da hasken rana a jihohin Arewa.
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya tabbatar da cewa an fara magana da yan kwangila kan yadda za a kafa wutar sola a Arewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng