Gwamnan APC Ya Yi Rigakafi, Ya Nemi Kotu ta Shiga Tsakinsa da EFCC tun kafin Ya Bar Ofis

Gwamnan APC Ya Yi Rigakafi, Ya Nemi Kotu ta Shiga Tsakinsa da EFCC tun kafin Ya Bar Ofis

  • Gwamnan Legas ya shiga damuwa kan yiwuwar jami’an hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) su yi ram da shi
  • Tuni gwamna Babajide Sanwo Olu ya fara daukar matakin riga-kafi, inda ya shigar da kara kotu na hana EFCC kama shi in ya bar ofis
  • Lauyan gwamnan da zai sauka a 2027, Darlington Ozurumba ne ya shigar da karar a madadinsa a gaban Mai Shari’a Joyce AbdulMalik

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos Gwamnan Legas, Babajide Sanwo Olu ya tsorata da barazanar da hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ke yi masa.

Kara karanta wannan

"Tinubu ba sai mun mutu ba:" Tsohon Sanata ya koka da manufofin tattalin arzikin APC

Gwamnan ya fara daukar matakin riga-kafi, inda ya garzaya kotu ya na neman a yi masa tsakani da jami’an hukumar EFCC idan wa’adinsa ya kare a matsayin gwamna.

Lagos
Gwamnan Legas ya nemi kotu ta hana EFCC damke shi idan ya kammala mulki Hoto: Babajide Sanwo Olu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamnan ya shigar da kara kotu ne ta hannun lauyansa, Darlington Ozurumba ya na neman Mai Shari’a Joyce AbdulMalik ta babbar kotun tarayya ta ba shi kariya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC: Dalilin gwamnan Legas na zuwa kotu

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa gwama Babajide Sanwo Olu na Legas ya shigar da kara ya na neman kotu ta hana jami’an EFCC kama shi ko gurfanar da shi a gaban shari’a idan ya gama mulki.

Lauyan gwamnan, Darlington Ozurumba ya shigar da karar a madadin Sanwo Olu domin kare shi daga duk wata tuhuma da EFCC ke shirin yi masa..

Kara karanta wannan

Ma'aikatan jami'a da suka shiga yajin aiki sun kawo sharadin komawa ofis

EFCC ba ta san gwamnan Legas yana yi ba

Lauyan hukumar EFCC, Hadiza Afegbua ta shaidawa kotu cewa ba su ga sabon kunshin tuhumar da gwamnan Legas, Babajide Sanwo Olu ya shigar gabanta ba.

Ta bayyana haka ne duk da Darlington Ozurumba ya shaidawa Mai Shari’a Joyce AbdulMalik cewa an mika kunshin sabuwar hukumar ga hukumar EFCC.

Gwamnan Legas ya rufe wuraren ibada

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Legas ta rufe masallatai da majami’u sama da 300 a fadin jihar a cikin shekarar da ta gabata bisa dalilin yawan hayaniya da gwamnati ta ce ba za ta lamunta ba.

Kafin garkame su, shugaban hukumar kare muhalli, Dr. Babatunde Ajayi ya ce sai da su ka gargadi dukkanin limamai da shugabannin da ke kula da wuraren ibada da su rage karar lasifikunsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.