'Yan Bindiga Sun Kori Mutanen Kauyuka 23 a kusa da Sansanin Sojoji
- Ƴan bindiga sun addabi mutanen wasu ƙauyukan da ke a ƙaramar hukumar Kontagora ta jihar Neja kwanan nan
- Ƴan bindigan sun kori mutanen aƙalla ƙauyuka 23 bayan sun addabe su da kai hare-haren ta'addanci ba ƙaƙƙautawa
- Ɗan majalisar da ke wakiltar Kontagora II, Abdullahi Isah ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 29 ga watan Oktoban 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja- Aƙalla ƙauyuka 23 ne a ƙaramar hukumar Kontagora ta jihar Neja, ƴan bindiga suka kori mutanen da ke cikinsu.
Rahotanni sun ce ƙauyukan da abin ya shafa na cikin filin horas da sojoji a ƙaramar hukumar Kontagora.
Dan majalisar da ke wakiltar Kontagora II a majalisar dokokin jihar Neja, Abdullahi Isah ne ya bayyana hakan, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun kori mutanen ƙauyuka a Neja
Abdullahi Isah ya bayyana hakan ne a wani ƙudiri da ya gabatar a yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Ya ce filin na sojoji ya taso ne daga ƙaramar hukumar Kontagora har zuwa wani yanki na ƙaramar hukumar Mariga.
Ya ƙara da cewa mutanen ƙauyukan da da abin ya shafa sun gudu saboda yawan hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa.
"Ƴan bindiga sun kafa aƙalla sansanoni daban-daban har guda takwas a yankin wanda a yanzu ya zama mafakar su."
"Hakan ya haifar da babbar barazana ta tsaro ga mutanen da ke ƙananan hukumomin Kontagora da Mariga."
- Hon. Aɓdullahi Isah
Ɗan majalisar ya ce wasu mazauna ƙauyukan da abin ya shafa waɗanda aka yi garkuwa da su a hare-haren na baya-bayan nan, har yanzu suna tsare a hannun ƴan bindiga.
Minista ya umarci kawo ƙarshen ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan tsaro, Mohammad Badaru Abubakar, ya umarci sojojin Operation Fansar Yamma da su kamo ƙasurgumin jagoran ƴan bindiga, Bello Turji.
Ministan ya bayar da wannan umarnin ne a lokacin da yake jawabi ga sojojin a hedikwatar Birged ta daya da ke birnin Gusau a jihar Zamfara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng