Shugaban Amurka Ya Kira Bola Tinubu Ta Wayar Tarho, An Faɗi Abin da Suka Tattauna
- Shugaban Amurka, Joe Biden ya kira shugaban Najeriya, Bola Tinubu ta wayar tarho da yammacin ranar Talata, 29 ga watan Oktoba
- Ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar ne ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Ya ce shugabannin sun tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi alakar ƙasashen biyu da batun kama wani jami'in Binance
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tattauna da shugaban Amurka, Joe Biden ta wayar tarho yau Talata, 29 ga watan Oktoba.
Shugaba Biden ya kira Tinubu ta wayar tarho ne da misalin ƙarfe 4:00 na yamma agogon Najeriya kuma sun ɗauki kusan mintuna 30 suna tattaunawa.
Ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan da Bola Tinubu ya tattauna da Biden
Tuggar ya ce shugabannin biyu sun tattauna sosai kan shugaban manhajar kirifto watau Binance, Tigran Gambaryan, wanda gwamnatin Najeriya ta saki kwanan nan.
Yusuf Tuggar ya ce:
"Kiran ya maida hankali ne kan alaƙar ƙasashen biyu game da hukumomin tabbatar da bin doka da oda da kuma sakin ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, shugaban manhajar hada-hadar kudin kirifto.
"Mai girma shugaban ƙasa ya kuma godewa Amurka bisa hadin gwiwa a fannoni da dama da suka shafi tsaro a Afirka da yammacin Afirka baki daya.
"Shugaba Biden ya ce wannan ƙawancen yana nan daram saboda goben duniya tana nan a nahiyar Afirka, don haka ƙulla alaƙa mai kyau tana da matuƙar muhimmanci."
Tinubu ya tunawa Biden batun kujera a MDD
Manyan shugabannin sun kuma tattauna kan batun warewa Afirka kujera ta dindindin a kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya, Punch ta ruwaito.
Biden ya tabbatar da cewa Amurka ta himmatu wajen ganin Afirka ta samu kujera ta dindindin kuma ba ta ga dalilin da zai sa a ce Najeriya ba ta da wuri ba.
Bola Tinubu ne ministan man fetur?
A wani labarin, an ji cewa fadar shugaban ƙasa ta musanta zargin cewa shugaba ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ministan man fetur a Najeriya.
Hadimin shugaban kasa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya ce ko da wasa Tinubu bai taɓa naɗa kansa a matsayin minista mai ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng