Nesa Ta Zo Kusa: Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Lokacin Gyara Lantarkin Arewa
- Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya yi ƙarin haske kan lokacin da za a gyara wutar lantarkin Arewacin Najeriya
- Adebayo Adelabu ya bayyana nan da kwana biyu zuwa uku za a maido da wutar lantarki a jihohin da matsalar ta shafa
- Ya kuma ba da tabbacin cewa za a kammala gyara matsalar wutar lantarkin nan da kwanaki 14 masu yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya bayyana lokacin da za a dawo da wutar lantarki a Arewacin Najeriya.
Adebayo Adelabu ya bayyana cewa za a dawo da wutar lantarki a Arewacin Najeriya nan da kwanaki uku masu zuwa.
Adelabu ya bayyana hakan ne a ranar Talata a lokacin da yake amsa tambayoyi daga ƴan majalisar dattawa dangane da matsalar wutar lantarki da ta addabi yankin Arewa, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe za a gyara wutar lantarkin Arewa?
Ministan ya bayyana cewa za a yi amfani da wani turken da ke samar da wuta na wucin gadi domin magance matsalar.
Ya bayyana cewa turken layin Ugwuaji-Makurdi da za a yi amfani da shi zai wadaci kaso 80% na jihohin da matsalar ta shafa.
Ya kuma bayyana cewa suna aiki tare da jami'an tsaro domin samun damar zuwa wajen turakun da aka lalata.
"Za a dawo da wutar lantarki a Arewa nan da kwana biyu zuwa uku. Za mu yi amfani da turken layin Ugwuaji-Makurdi na wucin gadi."
"Muna aiki tare da jami’an tsaro domin samun damar zuwa wajen turakun da ƴan bindiga suka mamaye a halin yanzu."
"Ina tabbatar muku cewa nan da kwanaki 14 masu zuwa za a kammala gyaran, kuma za a dawo da wutar lantarki gaba ɗaya a Arewa."
Kwankwaso ya samo mafita ga gwamnonin Arewa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi magana kan matsalar lantarki da ta shafi Arewacin Najeriya.
Rabi'u Kwankwaso ya buƙaci gwamnonin Arewa da su fara neman hanyoyin da za su fara samar da wutar lantarki a jihohi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng