Wahalar Fetur Ta Kare, Ɗangote Ya Kawo Mafita bayan Ganawa da Shugaba Tinubu
- Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote Group, Aliko Ɗangote ya ce matatarsa tana da isasshen fetur da zai kawar da dogon layi
- Attajirin ɗan kasuwar ya buƙaci kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL da ƴan kasuwa su daina shigo da mai daga ƙasashen ketare
- Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan ganawa da Bola Ahmed Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban matatar man Dangote, Aliko Dangote, ya ce matatarsa ita ce mafita ga dogayen layukan man fetur da ake fama da su a fadin kasar nan.
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka ya nemi kamfanin mai na Najeriya (NNPCL) da ‘yan kasuwa su daina shigo da mai daga ƙetare.
Ɗangote ya bayyana hakan ne yayin zantawa da ƴan jarida a fadar shugaban ƙasa jim kaɗan bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matatar Ɗangote na da isasshen mai
Hamshaƙin attajirin ya ce matatarsa na da karfin da za ta samar da adadin man da ƴan Najeriya ke buƙata a kowace rana, rahoton Punch.
“Abin da na kiyasta shi ne mutane na shan mai kusan lita miliyan 30-32 a kullum, kuma za mu fara samar da hakan nan da mako mai zuwa.
"Yanzu haka muna da lita miliyan 500 a ajiye, don haka ko da mun daina tace mai kuma an daina shigo da shi, sai mun ɗauki kwanaki 12 kafin ya ƙare.
"Mun gama shiri za mu samar da lita miliyan 30 a kullum, ba zai gagare mu ba don haka mun shiya tsaf."
-Aliko Ɗangote.
Ɗangote ya buƙaci NNPCL ya daina shigo a mai
Ɗangote ya ƙara da cewa yana fatan daga yanzun NNPCL da ƴan kasuwa za su daina shigo da mai daga ƙasashen ketare domin yana da duk abin da suke buƙata.
"Ban sani ba ko kun fahimci abin da ake nufi da ajiye lita miliyan 500, suna ci mani karin kudi amma da za su zo su saya a hannu na, ba za ku sake ganin layi a gidan mai ba," in ji shi.
Ɗangote ya magantu kan shari'a da NNPCL
A wani labarin, an ji cewa Dangote ya yi magana kan karar da ya shigar a babbar kotun tarayya na hana NNPCL da 'yan kasuwa shigo da mai.
A ranar 6 ga Satumbar 2024 ne Dangote ya shigar da hukumar NMDPRA kara gaban kotun kan ba kamfanonin lasisin shigo da mai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng