TCN: Yadda Yan Bindiga Suka Hana Gyaran Wutar Arewa

TCN: Yadda Yan Bindiga Suka Hana Gyaran Wutar Arewa

  • Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya shirya taro na musamman domin yin bayanai kan rashin lantarki a Arewa
  • Shugaban TCN, Injiniya Sule Ahmed Abdulaziz ya bayyana yadda injiniyoyi suke fama da yan bindiga a wajen gyaran turakan wuta
  • Tun a watan Satumba babban turken wutar lantarki da ya shigo da wuta jihohin Arewa ya samu matsala amma ba a samu gyara shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanin rarraba wuta na kasa (TCN) ya shirya taro domin bayyana halin da ake ciki kan gyaran lantarki a Arewa.

Kamfanin TCN ya bayyana cewa duk da matsalolin da yake fuskanta yana cigaba da ƙoƙarin gyaran wutar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fitar da sabon tsarin samar da lantarki a Arewa

Lantarki
TCN ya bayyana yadda ya yi fama da yan bindiga. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Legit ta tatttaro bayanan da TCN ya yi ne a cikin wani sako da kamfanin ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe layin wutar Arewa ya lalace?

Shugaban TCN, Injiniya Sule Ahmed Abdulaziz ya ce tun a ranar 9 ga Satumba layin wuta na Shiroro ya samu matsala.

Bincike ya nuna cewa layin wutar Shiroro-Mando 330kV shi ne mai ba mafi yawan jihohin Arewacin Najeriya lantarki.

Menene ya hana gyaran wutar Arewa?

Injiniya Sule Ahmed Abdulaziz ya bayyana cewa sun dade ga gano matsalar amma rashin tsaro ya hana su gyara.

Shugaban TCN ya kara da cewa yan bindiga da suke yankin sun hana jami'ansu samun damar gyaran.

"Mun yi amfani da yan banga domin zuwa mu gyara wutar da daddare domin kaucewa yan bindiga.
Sai dai cikin rashin sa'a yan bindigar sun gano dabarar da muka yi, sai suka cigaba da mana barazana."

Kara karanta wannan

Bayan Arewa ta shafe sama da mako 1 a duhu, Tinubu ya ba da umarnin gaggawa

- Injiniya Sule Ahmed Abdulaziz, shugaban TCN

Jawabin ministan makamashi

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya jaddada cewa TCN za ta cigaba da kokari domin samar da lantarki a Najeriya.

Ya kuma yi kira na musamman ga yan kasa kan su cigaba da taimakon gwamnati wajen lura da turakan wuta a Najeriya.

Za a saka sola a jihohin Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fara ƙoƙarin samar da wuta mai amfani da hasken rana a Arewacin Najeriya.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa samar da wutar sola a Arewacin Najeriya zai rage lodi ga tushen wuta na kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng