Zanga Zanga Ta Barke a Hedkwatar INEC, Bayanai Sun Fito
- Matasa masu zanga-zanga sun mamaye hedkwatar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ke birnin tarayya Abuja
- Masu zanga-zangar sun buƙaci shugaban INEC ya sauya kwamishiniyar INEC, Oluwatoyin Babalola daga jihar Ondo
- Sun bayyana cewa suna son a sauya mata wurin aiki ne saboda a yi gaskiya da adalci a zaɓen gwamnan jihar da ke tafe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Masu zanga-zanga da dama daga jihar Ondo sun mamaye hedkwatar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ke Abuja a ranar Talata.
Masu zanga-zangar sun buƙaci a gaggauta sauya kwamishiniyar hukumar INEC ta jihar Ondo, Misis Oluwatoyin Babalola.
An yi zanga-zanga a hedkwatar INEC
Jaridar The Punch ta rahoto cewa masu zanga-zangar sun riƙa ɗaga tutoci da kwalaye masu ɗauke da rubuce-rubuce daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu daga cikin rubuce-rubucen na cewa 'Mahmood: ka sauya Oluwatoyin Babalola yanzu' da 'Ba mu so a maimaita abin da ya faru a Edo'.
Masu zanga-zangar sun kuma tare ƙofar shiga hedkwatar, inda suka buƙaci ganawa da shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu domin bayyana damuwarsu, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Wace buƙata masu zanga-zangar ke nema?
Shugaban masu zanga-zangar, Ayo Adeyemi, ya shaida wa manema labarai cewa, duk da cewa ba su da wata matsala da kwamishiniyar, ba za su iya yin kasada kan bari a nuna son kai a zaɓen mai zuwa ba.
"Sauya wurin aiki ga Oluwatoyin Babalola shi ne mafi alheri ga jama’armu da kuma INEC domin tabbatar da sahihin zaɓe."
"Muna buƙatar INEC ta sauya Oluwatoyin Babalola daga jihar. Muna mutunta nasarorin da ta samu, musamman a matsayinta na macen da ta kai wannan matsayin."
"Amma domin a yi sahihin zaɓe a Ondo, ba za mu yarda Oluwatoyin Babalola ta jagoranci ragamar al'amura ba. A nan ta girma, ta san kowa a ɓangaren gwamnati kuma ta san jihar sosai."
- Ayo Adeyemi
SERAP ta kai shugaban INEC ƙara
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta kai ƙarar shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu a gaban kotu.
Ƙungiyar SERAP ta kai shugaban na INEC ƙara a gaban kotu ne bisa rashin binciken laifukan zaɓe da ake zargin an yi a zaɓen shekarar 2023.
Asali: Legit.ng