Gwamna Ya Ɗauki Zafi, Ya Bada Umarnin Rufe Makaranta bayan Mutuwar Wani Ɗalibi

Gwamna Ya Ɗauki Zafi, Ya Bada Umarnin Rufe Makaranta bayan Mutuwar Wani Ɗalibi

  • Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya ba da umarnin rufe makarantar Obada Grammar bayan ɗalibin ajin SS2 ya mutu
  • A wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Lekan Adeniran ya fitar ya ce za a kafa kwamitin da zai gudanar da bincike
  • Ma'aikatar ilimi ta jihar Ogun ta tura wakilai zuwa gidansu ɗalibin domin yi masu ta'aziyya da kuma tattara wasu bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun - Gwamnatin jihar Ogun ta rufe makarantar Obada Grammar School da ke Obada sakamakon mutuwar dalibin SS2, Monday Arijo.

Hakan dai na zuwa ne bayan kamawa tare da dakatar da malamin da ake zargi da hannu a mutuwar dalibin a ranar Juma’ar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Tsautsayi ne: Malamin sakandare ya yi ajalin dalibinsa ta hanyar tsula masa bulala

Gwamna Dapo Abiodun.
Gwamnan Ogun ya rufe makaranta bayan ɗalibi ya mutu Hoto: Prince Dapo Abiodun
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, malamin da ake zargin ya yi ajalin ɗalibin ne ta hanyar hukunci mai tsanani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya dakatar da shugabar makaranta

Gwamnatin Ogun ta kuma dakatar da shugabar makarantar, Misi Tamrat Onaolapo, wadda ta bari aka azbtar da ɗalibin har ya wuce ƙima.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren wataa labaran Gwamna Dapo Abiodun, Lekan Adeniran ya rabawa manema labarai ranar Talata.

"Gwamna Dapo Abiodun ya ba da umarnin rufe makarantar tare da kafa kwamitin da zai gudanar da bincike don gano yadda lamarin ya auku.
"Gwamna ya yi alƙawarin cewa duk wanda aka kama da laifi a binciken da za a gudanar zai ɗanɗana kuɗarsa, babu ɗaga kafa dole doka ta yi aiki a kansa."

Gwamnatin Ogun ta tura wakilai gidansu mamacin

Kara karanta wannan

Rigima ta kauren tsakanin wasu sarakuna kan yankunan da suke mulki a Najeriya

A ruwayar Daily Trust, wakilan ma'aikatar ilimi, kimiya da fasaha ta jihar Ogun sun ziyarci iyalan marigayi dalibin da aka kashe a makarantar.

Ma'aikatar ilimin ta kai wannan ziyara ne domin yi wa ƴan uwan ɗalibin ta'aziyya da kuma tattara wasu bayanai da za su iya taimakawa a binciken da ake yi.

Gwamna Abiodun ya faɗi amfanin cire tallafi

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya bayyana amfanin cire tallafin mai da Bola Tinubu ya yi a Najeriya.

Abiodun ya ce cire tallafin zai taimaka wurin habaka tattalin arziki wanda zai shafi dukan bangarorin kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262