'Ya Fasa Motar Yan Sanda,' An Kama Babban Dan Daba a Kano, Gundura
- Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Kano ta samu nasara a kan wasu tarin yan daba da ake zargi da aikata manyan laifuffuka
- Cikin wadanda aka kama akwai babban dan daba da aka fi sani da Gundura wanda shi ake zargi da jagorantar ayyukan daba a Kano
- Kakakin yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fadi matakin da za a dauka a kan wadanda aka kama bayan kammala bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rundunar yan sandan jihar Kano ta samu nasara kan wani babban dan daba mai suna Gundura da ake nema ido rufe.
A cikin wani samame da rundunar ta fita, ta yi nasarar cafke karin yan daba har 14 a wasu wurare.
Legit ta gano nasarar da rundunar yan sandan ta samu ne a cikin wani sako da SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama dan daba Gundura a Kano
Rundunar yan sanda ta sanar da cafke babban dan daba, Inuwa Zakari da aka fi sani da suna Gundura.
Yan sanda sun ce Gundura ya shigo Kano ne da niyyar tayar da rikici a lokacin zaben kananan hukumomi da ya gudana a jihar.
Gundura ya fasa motar yan sanda
SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa akwai lokacin da Gundura ya fasa motar yan sanda a jihar Kano.
"Na fasa motar yan sanda amma ƙaddara ce ta jawo na aikata hakan.
Kuma ina jagorantar yan daba sama da 20 amma ba lallai na iya gano su duka ba"
- Gundura, dan daba
Ana zargin Gundura da jagorantar yan daba a unguwar Ɗorayi a jihar Kano kuma a unguwar aka kama shi a wata matattarar yan daba da suke kira Jungle.
An kama wasu yan daba a Kano
A tsakanin 25 zuwa 27 ga Oktoba yan sanda sun kama yan daba 14 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya nuna da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban alkali domin a hukunta su.
An kama dan majalisa a Abuja
A wani labarin, rundunar yan sanda ta kama dan majalisar tarayya bisa zargin cin zarafin wani mai aikin tasi a birnin tarayya Abuja.
Ana zargin dan majalisar wakilan da aka kama da zabgawa matukin motar tasi mari uku bayan sun samu sabani a lokacin da ya kawo masa kaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng