Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban NDLEA Rasuwa

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban NDLEA Rasuwa

  • Allah ya yi wa tsohon shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA), Fulani Kwajafa rasuwa
  • Rahotanni daga iyalan gidan Kwajafa sun nuna cewa ya rasu yana da shekara 88 a duniya bayan fama da gajeruwar jinya
  • Marigayin ya taka muhimmiyar rawa a rundunar ƴan sandan Najeriya kafin daga bisani a naɗa shi a matsayin shugaban NDLEA a 1991

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno - Tsohon shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa watau NDLEA, Fulani Kwajafa, Sarkin Yakin Biu ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne yana da shekara 88 a duniya bayan fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya.

Fulani Kwajafa.
Tsohon shugaban NDLEA, Fulani Kwajafa, ya rasu yana da shekaru 88 Hoto: Fulani Kwajafa, @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

Rahoton da Leadership ta wallafa yau Litinin ya nuna cewa Fulani Kwajafa ya rasu ne tun makon jiya ranar 23 ga watan Oktoba, 2024.

Kara karanta wannan

"Na yi shekara 3 da rabi a cikin mahaifiyata": Tsohon gwamna ya fadi abin al'ajabi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban NDLEA ya rasu

Ɗaya daga cikin iyalan gidansa ne ya tabbatar da rasuwar tsohon shugaban NDLEA ta ƙasa.

Marigayi Fulani Kwajafa ya rasu ya bar matarsa, Patience Kwajafa da ƴaƴa da jikoki da dama.

Daga cikin ƴaƴan da ya rasu ya bari akwai Nuhu Fulani Kwajafa, MFR, Darakta Janar na kamfanin Global Initiative for Peace, Love and Care (GIPLC).

Taƙaitaccen tarihin Fulani Kwajafa

An haifi Fulani Kwajafa a ranar 22 ga Disamba, 1936, a kauyen Kwajafa, karamar hukumar Hawul ta jihar Borno da ke Arewa maso Gabas a Najeriya.

Ya gama makarantar firamare a garin Kwajafa a 1953, yayin da a shekarar 1954 ya fara aiki da rundunar ‘yan sandan Nijeriya a matsayin kurtun dan sanda.

A bisa jajircewa da sadaukar da kansa ga aiki, marigayin ya taka rawar gani har ta kai ga ya dauki hankalin hukumar ‘yan sandan tun a lokacin mulkin mallaka.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya gana da ƴan majalisar tarayya na NNPP, an nemi mutum 3 an rasa

Daga nan ne aka zabe shi don ya halarci Kwalejin Mayflower da ke Landan, domin ƙaro karatu wanda zai taimaka masa wajen aikinsa na tabbatar da doka.

An naɗa Fulani Kwajafa a matsayin shugaban NDLEA a 1991, inda ya sa kafar wando ɗaya da masu ta'amali da miyagun ƙwayoyi.

Babban ɗan kakakin gwamna ya rasu

A wani rahoton kuma mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya yi rashin babban ɗansa, Sadiq Modibbo

Sanusi ya bayyana cewa Sadiq ya rasu ne bayan fama da ciwon sikila kuma za a dawo da shi gida domin jana'iza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262