Rashin Tsaro: Gwamnonin Arewa Sun Sanya Labule da Hafsun Tsaro, Sarakunan Gargajiya
- Gwamnonin jihohin Arewa sun gudanar da taro kan matsalolin da suka daɗe suna ci wa yankin tuwo a ƙwarya
- An yi zaman ne babban hafsan tsaro (CDS) Christopher Musa da sauran manyan sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki
- Christopher Musa ya yi bayanin ƙoƙarin da sojoji ke yi domin kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga da ƴan ta'adda a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun gana da sarakunan gargajiya na yankin a jihar Kaduna.
Gwamnonin na yankin Arewa sun yi taron ne inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi yankin.
Tashar Channels tv ta rahoto cewa an gudanar da taron ne a ranar Litinin a gidan gwamnatin jihar Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin Arewa sun yi taro a Kaduna
Taron dai na ɗaya daga cikin ƙoƙarin gwamnonin ke yi na yin tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin magance matsalolin da suka addabi yankin.
Mutanen Arewa na fama da tabarbarewar tsaro, fatara da yaran da ba su zuwa makaranta.
Taron da Gwamna Uba Sani ya zama mai masauki baƙi, ya kasance ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya.
Gwamnoni da Sarakunan Arewa da suka je taron
Taron ya samu halartar gwamnonin Kaduna, Gombe, Zamfara, Nasarawa, Borno, Borno, Bauchi, Kwara da Adamawa.
Haka kuma akwai mataimakan gwamnonin wasu jihohin Arewa a wajen taron.
Babban hafsan sojoji (CDS), Janar Christopher Musa shi ma ya halarci taron ya kuma bayyanawa gwamnonin ƙoƙarin da sojoji ke yi domin magance matsalar ƴan bindiga da sauran matsalolin tsaro da suka addabi yankin Arewa.
Sarakunan gargajiya da suka halarci taron sun haɗa da Sarkin Musulmi Abubakar Saad, Shehun Borno, Umar El-Kanemi, Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamali.
Akwai Ohinoyi na Ebira, Etsu Nupe, Yahaya Abubakar, Sarkin Kazaure da Sarkin Bauchi.
Ƴan Arewa sun caccaki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya fara shan suka kan umarnin da ya ba ministocin na rage tawaga da jami'an tsaro.
Kungiyar League of Northern Democrats ta ce babu alamar cewa shugaban kasar da gaske yake kan umarnin da ya bayar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng