Kotu Ta Dawo da Babban Sarkin Arewa da Gwamna Ya Sauke

Kotu Ta Dawo da Babban Sarkin Arewa da Gwamna Ya Sauke

  • Kotun daukaka kara a jihar Sokoto ta soke sauke sarkin Gwandu, Alhaji Mustapha Jokolo da aka yi shekaru 20 da suka wuce
  • Alkalin kotun, mai shari'a Ibiowei Tobi ya bayyana dalilan da suka sanya shi soke sauke sarkin da gwamnatin jihar ta yi a 2005
  • Bangarorin gwamnatin Kebbi da sarkin da aka tube za su tunkari kotun koli domin yanke hukunci na karshe kan shari'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Alkalin kotun daukaka kara ya yanke hukunci kan tube sarkin Gwandu da gwamnatin Kebbi ta yi.

Mai shari'a Ibiowei Tobi ne ya yanke hukuncin yayin zaman kotu a jihar Sokoto bayan gwamnatin Kebbi ta daukaka kara.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kasa da awanni 24 kafin zaben Ciyamomi a jihar Kano

Kebbi
Kotu ta soke tube sarkin Gwandu. Hoto: Nasir Idris
Asali: Twitter

RFI Hausa ta ruwaito cewa a yanzu haka za a koma gaban kotun ƙoli domin kammala shari'ar a nan gaba kadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dawo da sarkin Gwandu da gwamna ya tube

Wata kotun daukaka kara ta yanke hukuncin dawo da sarkin Gwandu na 14, mai martaba Mustapha Haruna Jakolo kan karagar mulki bayan gwamnati ta sauke shi.

Gwamnatin jihar Kebbi ce ta daukaka ƙara gaban kotun domin neman halasta sauke sarkin da ta yi a baya.

Dalilin dawo da sarkin Gwandu - Kotu

Alkalin kotun, mai shari'a Ibiowei Tobi ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kebbi ba ta bi ƙa'ida ba wajen sauke sarkin a karon farko.

Tun a farko dai babbar kotun jihar Kebbi ta yanke hukuncin cewa gwamnatin ba ta bi ƙa'idar sauke sarkin ba a karaga.

Za a cigaba da shari'ar sarkin Gwandu

Kara karanta wannan

An zo wurin: Kotu ta yi zama kan zargin Ganduje da almundahana, ta shirya yanke hukunci

Rahotanni sun nuna cewa bayan kotun daukaka kara ta yanke hukunci za a daukaka shari'a tsakanin sarkin da gwamnatin Kebbi.

Ana sa ran cewa za a cigaba da shari'ar a kotun ƙoli ne kuma daga nan za a yanke hukunci na karshe.

21st Century Chronicle ta ce a 2005 gwamnatin Kebbi ta wancan lokacin ta sauke mai martaba Mustapha Haruna Jakolo.

Sarakuna na rigima a Osun

A wani rahoton, kun ji cewa rigima ta kaure tsakanin wasu sarakunan gargajiya a jihar Osun a game da kauyukan da ke karakashin masarautunsu.

Rahotanni sun bayyana cewa an bukaci Gwamna Ademola Adeleke ya kira zama na musamman domin a warware takaddamar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng