Betta Edu: Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Matsayin Ministar da Tinubu Ya Dakatar

Betta Edu: Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Matsayin Ministar da Tinubu Ya Dakatar

  • Fadar shugaban ƙasa ta yi ƙarin haske kan kujerar Betta Edu da shugaba Bola Tinubu ya dakatar daga muƙamin minista
  • Hadimin Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa an sallami tsohuwar ministar ta jinƙai daga kan muƙaminta
  • Bayo Onanuga ya yi nuni da cewa akwai yiwuwar EFCC ta ba da wasu bayanai waɗanda suka taimaka wajen sallamarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta bayyana makomar kujerar Betta Edu da shugaba Bola Tinubu ya dakatar daga muƙamin ministar jinƙai.

Hadimin shugaban ƙasa kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya ce bisa garambuwal ɗin da Tinubu ya yi wa majalisar ministocinsa, a hukumance an sallami Betta Edu daga muƙaminta.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sanya labule da Kashim Shettima, an samu bayanai

Tinubu ya kori Betta Edu
Fadar shugaban kasa ta tabbatar da korar Betta Edu Hoto: @OfficialABAT, @edu_betta
Asali: Facebook

Bayo Onanuga ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar talabijin Channels tv a shirinsu na 'Sunday Politics' a ranar Lahadi, 27 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya sallami Betta Edu

Onanuga ya bayyana cewa an kulle babin yiwuwar dawowar Betta Edu kan muƙaminta.

"Betta Edu ta tafi. An dakatar da ita a watan Janairu kuma yanzu muna Oktoba. A hukumance ta tafi. Muƙaminta ya koma hannun mutumin jihar Plateau (Nentawe Yilwatda)."
"A wajen gwamnatin nan, ba ta da sauran gurbi a wannan majalisar ministocin."

- Bayo Onanuga

Meyasa Tinubu ya kori Betta Edu

Onanuga ya ƙara da cewa wataƙila hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta miƙa wasu bayanai da suka taka rawar gani wajen korar ta.

An dakatar da Betta Edu ne bisa zarginta da hannu wajen amincewa da fitar da N585,198,500.00 zuwa wani asusu.

Kara karanta wannan

Betta Edu ta faɗi abin da ta hango a mulkin Tinubu bayan an koreta daga minista

A ranar Alhamis ne Tinubu ya maye gurbin Betta Edu, ya naɗa Nentawe Yilwatda, haifaffen jihar Plateau kuma malami a jami’ar noma ta tarayya da ke Makurdi a jihar Benue.

An soki Tinubu kan korar minista

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiya a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, mai suna NAGG ta yi magana kan korar Abdullahi T. Gwarzo daga muƙamin minista.

Ƙungiyar ta bayyana cewa abin takaici ne saka sunan Abdullahi Gwarzo a cikin ministocin da shugaba Bola Tinubu ya sallama daga aiki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng