T Pain: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani kan Sabon Sunan Tinubu

T Pain: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani kan Sabon Sunan Tinubu

  • Hadimin shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya ce Bola Tinubu yana sane da halin da ƴan Najeriya suke ciki
  • Onanuga ya bayyana cewa Tinubu ba T-pain ba ne kamar yadda wasu suke yi masa laƙabi a kafafen sada zumunta
  • Ya bayyana cewa shugaban ƙasan yana aiki tuƙuru domin ganin ya tsamo ƴan Najeriya daga cikin halin ƙuncin da suka tsinci kansu a ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Shugaba Bola Tinubu, ba mara tausayi ba ne kamar yadda wasu mutane suke kiransa a shafukan sada zumunta. 

Bayo Onanuga ya ce Shugaba Tinubu yana jin zafin raɗaɗin da ƴan Najeriya ke sha kuma ya ba su tabbacin cewa nan ba da jimawa abubuwa za su gyaru.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sanya labule da Kashim Shettima, an samu bayanai

Fadar shugaban kasa ta kare Tinubu
Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu ba T-pain ba ne Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Hadimin na Tinubu kan yaɗa labarai da dabaru ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Sunday Politics' a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ba T-pain ba ne

Onanuga ya ce shugaban ƙasan ​​ba T-pain ba ne, kamar yadda ake yi masa laƙabi a kafafen sada zumunta.

Onanuga ya ce Tinubu bai zo domin ya jefa ƴan Najeriya cikin wahala ba sai don ya gyara tattalin arziƙin ƙasar nan.

Ya bayyana cewa Tinubu bai san cewa wasu ƴan Najeriya na yi masa laƙabi da T-pain ba, saboda ba ya karanta abin da yake a shafukan sada zumunta.

"Wasu mutanen saboda rashin kirki sai su ce wani T-pain ne. Tinubu ba T-pain ba ne."
"Shugaban ƙasan bai taɓa fasa gayawa ƴan Najeriya cewa yana jin zafin raɗaɗin da suke sha kuma yana aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa sun samu sauƙi ta yadda abubuwa za su gyaru sannan ƙasar nan ta samu ci gaba."

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa kansa a matsayin Minista? Gaskiya ta bayyana

- Bayo Onanuga

Tinubu ya ba ƴan Najeriya shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta yi kira ga ƴan Najeriya su rungumi noma ido rufe domin magance tashin farashin kayan abinci da ake fuskanta a kasar.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ne ya yi wannan kiran yayin taron da ya yi da wata kungiyar editocin yanar gizo ta ACOE a Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng