Garambawul: Kungiya Ta Soki Korar da Tinubu Ya Yi Wa Wani Minista

Garambawul: Kungiya Ta Soki Korar da Tinubu Ya Yi Wa Wani Minista

  • Wata ƙungiya ta fito ta nuna adawa kan korar Abdullahi T. Gwarzo daga cikin majalisar ministocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Ƙungiyar NAGG ta bayyana cewa shugaban ƙasan ya yi kuskure wajen sallamar ƙaramin ministan na gidaje da raya birane daga kan muƙaminsa
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa tsohon ministan na daga cikin masu yin aiki tuƙuru domin cimma manufofin gwamnatin Shugaba Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wata ƙungiya a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, mai suna NAGG ta yi magana kan korar Abdullahi T. Gwarzo daga muƙamin minista.

Ƙungiyar ta bayyana cewa abin takaici ne saka sunan Abdullahi Gwarzo a cikin ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya sallama daga aiki.

Kara karanta wannan

Jerin sababbin ministocin da Tinubu ya nada da jihohin da aka dauko kowannensu

An soki korar Abdullahi Gwarzo daga minista
Kungiya ta soki korar Abdullahi Gwarzo da Tinubu ya yi Hoto: @ATMgwarzo
Asali: Twitter

Jagoran ƙungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma, Kwamared Auwal Shuaibu ya bayyana haka a ranar Lahadi yayin da yake zantawa da manema labarai, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An soki Tinubu kan korar Abdullahi Gwarzo

Kwamared Auwal Shuaibu ya nuna rashin jin daɗinsa kan cire tsohon ƙaramin ministan gidaje da raya biranen daga muƙaminsa.

"Duk da cewa mun yarda cewa haƙƙin shugaban ƙasa ne ya zaɓi waɗanda zai yi aiki da su, cire Abdullahi T. Gwarzo babban kuskure ne daga ɓangaren shugaban ƙasa."
"Idan akwai wani ƙaramin minista da ke aiki tukuru don ganin an samu nasarar manufofin Tinubu, to babu kamar Abdullahi T. Gwarzo."
"Ya zarce wasu manyan ministoci a wasu ma'aikatu ta fuskar tsara manufofi da gudanar da ayyukansu."

- Kwamared Auwal Shuaibu

Karanta wasu labaran kan garambawul ɗin Tinubu

Kara karanta wannan

Jerin ministocin da Tinubu ya kora daga aiki da jihohin da suka fito a Najeriya

Tinubu ya tura saƙo ga tsofaffin ministoci

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya godewa ministocin da ya kora daga aiki bisa gudummuwar da suka ba gwamnatinsa da ƙasa baki ɗaya.

Shugaban ƙasar ya yi masu fatan alheri a dukkan lamurran da za su sa a gaba, inda ya ce Najeriya ba za ta manta da hidimar da suka yi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng