Jigo a PDP Ya Fadi Dalilin Tinubu Na Nada Matar Ojukwu Mukamin Minista

Jigo a PDP Ya Fadi Dalilin Tinubu Na Nada Matar Ojukwu Mukamin Minista

  • Jigo a PDP Austin Okai ya ce naɗin Bianca Ojukwu da Mohammed Maigari Dingyadi a matsayin ministoci bai cancanta ba kuma an yi ne kawai don siyasa
  • A wata hira da Legit.ng ta yi da shi, Okai ya ce bisa naɗin Bianca Ojukwu, Tinubu da jam’iyyar APC na da burin ƙara ƙarfi a yankin Kudu maso Gabas gabanin zaɓen 2027
  • Tinubu a garambawul ɗin da ya yi, ya kori ministoci biyar, ya kuma amince da naɗin Bianca Ojukwu da wasu mutum shida a matsayin sababbin ministoci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Austin Okai, ɗan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar PDP a mazaɓar Dekina/Bassa ta jihar Kogi a zaɓen 2023, ya yi magana kan sababbin ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya buƙaci Shugaba Tinubu ya ƙara korar wasu ministoci daga aiki

Austin Okai ya bayyana cewa naɗin da Tinubu ya yi wa Bianca Ojukwu a matsayin minista bai cancanta ba.

Jigon PDP ya soki nadin Bianca Ojukwu
Jigon PDP ya soki nadin da Bola Tinubu ya yi wa Bianca Ojukwu
Asali: Facebook

Okai ya maida martani kan naɗin Bianca Ojukwu

Ku tuna cewa a ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya yiwa majalisar ministocinsa garambawul inda ya kori ministoci biyar, ya kuma sakewa ministoci 10 ma'aikatu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya kuma naɗa sababbin ministoci bakwai waɗanda ya miƙa sunayensu ga majalisar dattawa domin tabbatar da su.

A wata hira ta musamman da Legit.ng ta yi da shi a ranar Lahadi, 27 ga watan Oktoba, Okai ya ce naɗin Bianca Ojukwu an yi shi ne domin ƙara ƙarfin APC a yankin Kudu maso Gabas.

Da yake ƙarin haske, Okai ya nuna shakku kan matakin da Tinubu ya ɗauka na naɗa tsohon ministan Muhammadu Buhari, Mohammed Maigari Dingyadi, inda ya ce ko a baya bai taɓuka komai ba.

Kara karanta wannan

Matawalle: Dalilin Tinubu na barin minista da ake zargi da "daukar nauyin 'yan bindiga"

"Ana ci gaba da yin kira da a ƙara ƙwararrun masana a fannoni masu muhimmanci kamar kuɗi, kasafin kuɗi, da tsare-tsare na ƙasa."
"An nuna damuwa game da naɗin Mohammed Maigari Dingyadi, wanda a wa’adinsa a gwamnatin da ta gabata bai yi komai ba, da kuma Bianca Ojukwu, wacce ake ganin an naɗata ne saboda dalilai na siyasa maimakon cancanta."
"Ana kallon naɗin Bianca Ojukwu a matsayin wani yunƙuri na ƙarfafa dangantakar siyasa da yankin Kudu maso Gabas."

- Austin Okai

Malami ya soki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya ce ba an ba Shugaban Bola Ahmed Tinubu gurguwar shawara kan korar ministoci biyar.

Primate Ayodele ya dage cewa shugaban ya sauke ministocin da ba su ya kamata a ce ya sallama daga aiki ba a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng