Shugaban INEC Ya Shiga Matsala bayan SERAP Ta Kai Shi Kara Kotu

Shugaban INEC Ya Shiga Matsala bayan SERAP Ta Kai Shi Kara Kotu

  • Ƙungiyar SERAP ta sake taso shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubua gaba
  • Ƙungiyar SERAP ta shigar da shugaban na INEC ƙara a gaban babbbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja
  • An kai ƙarar Farfesa Mahmood Yakubu ƙara a gaban kotun ne saboda ƙin bin umarnin kotu na bincikar zargin laifukan zaɓe a zaɓen 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar SERAP ta kai ƙarar shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu a gaban kotu.

Ƙungiyar SERAP ta kai shugaban na INEC ƙara a gaban kotu ne bisa rashin binciken laifukan zaɓe da ake zargin an yi a zaɓen shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya sa doka a Kano ana dab da fara zaɓen ƙananan hukumomi

SERAP ta kai shugaban INEC kara
SERAP ta kai.karar shugaban hukumar INEC Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

SERAP ta kai ƙarar shugaban INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar SERAP ta sanar da shigar da shugaban na INEC ƙara a gaban kotu ne a shafinta na X.

Ƙungiyar SERAP ta ce duk da umarnin kotu da mai shari’a Obiora Egwuatu na babbar kotun tarayya, Abuja, ya bayar a ranar 18 ga watan Yuli, 2024, na bincikar laifukan zaɓen, INEC ta gaza ko kuma ta ƙi aiwatar da hukuncin.

Sai dai ba a sanya ranar da za a saurari ƙarar ba.

Kotu ta gargaɗi shugaban INEC

Babbar kotun tarayya da ke Abuja a cikin sanarwar abin da zai faru sakamakon bijirewa umarnin kotu ta gargaɗi Farfesa Yakubu cewa zai kasance mai laifin wulakanta kotu kuma za a kai shi gidan yari idan ya kasa bin umarnin kotun.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Ka lura cewa, idan ba ka bi umarnin da ke kunshe cikin hukuncin da mai shari'a Egwuatu ya yanke a ranar 18 ga watan Yuli 2024 ba, za ka kasance da laifin raina kotu kuma za a kai ka gidan yari."

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta yi hukunci kan yunkurin dakatar da zaben ciyamomi

Jami'an DSS sun mamaye ofishin SERAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun karbe ikon ofishin kungiyar kare hakkin al’umma da tattalin arzikin kasa (SERAP) da ke babban birnin tarayya Abuja.

Mamaye ofishin SERAP da jami'an DSS suka yi na zuwa ne awanni bayan da kungiyar ta nemi Shugaba Bola Tinubu ya janye karin kudin fetur da kuma bincikar NNPCL.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng