Gwamna Abba Ya Fadi Amfanin da Zababbun Ciyamomi Za Su Yi a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce zai samar da ayyukan yi ga ɗimbin matasan da ke zaman kashe wando
- Gwamna Abba ya bayyana cewa zai yi aiki tare da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin domin cimma hakan
- Ya nuna cewa ya yi ayyuka sosai a yankunan karkara kuma zai ci gaba musamman yanzu da aka samu zaɓaɓɓun ciyamomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin yin amfani da damar samun zaɓabbun ciyamomi a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar 44, domin magance matsalar rashin aikin yi na matasa.
Gwamna Abba ya yi magana ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi ranar Asabar.
Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba zai ci gaba da ayyuka a Kano
Gwamna Abba ya ce gwamnatinsa ta yi abubuwa masu yawa duk da ba zaɓaɓɓun ciyamomi, inda ta ƙaddamar da ayyukan raya kasa da dama a faɗin kananan hukumomi 44.
"Ina ganin mutanen karkara ne suka fi kowa sa’a kan abubuwan da muke yi duk da ba zaɓaɓɓun ciyamomi."
"Yanzu da muke zaɓar ciyamomi za su samu mutanen da za su yi magana da su kai tsaye, saboda haka za a samu ci gaba sosai."
"Saƙona ga jama’a shi ne su kasance cikin shiri don samun karin ci gaba a jihar musamman ta fuskar lafiya, ilimi, noma da samar da aiki musamman ga matasan mu maza da mata da suka daɗe suna neman aikin yi."
"Ina tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar Kano tare da dukkanin ƙananan hukumomi 44 za su kula da lafiyarsu, tsaro da duk abin da ya kamace su."
- Abba Kabir Yusuf
NNPP ta lashe zaɓe a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano watau KANSIEC ta sanar da sakamakon zaɓen kananan hukumomin da aka yi a ranar Asabar, 26 ga watan Oktoban 2024.
Hukumar KANSIEC ta bayyana cewa jam'iyyar NNPP ta samu nasarar lashe dukkan kujerun ciyamomi 44 da kansiloli 484 na jihar Kano.
Asali: Legit.ng