An Shiga Jimami bayan Gini Ya Rufto kan Mutane Masu Yawa a Abuja

An Shiga Jimami bayan Gini Ya Rufto kan Mutane Masu Yawa a Abuja

  • Wani ibtila'i ya auku a unguwar Sabon Lugbe da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Asabar, 26 ga watan Oktoban 2024
  • Wani gini wanda ba a kammala ba ya rufto kan mutane masu yawa inda ake fargabar aƙalla mutum 40 sun maƙale a cikinsa
  • Masu aikin ceto sun garzaya inda lamarin ya auku yayin da suke ƙoƙarin kuɓutar da mutanen da suka maƙale a cikin ɓuraguzai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Aƙalla mutane 40 ne ake fargabar sun maƙale bayan ruftawar wani gini a ranar Asabar a unguwar Sabon Lugbe da ke babban birnin tarayya Abuja.

Masu jimami da ma'aikatan ceto na gaggawa suna aikin ceto waɗanda har yanzu suke maƙale a ƙarƙashin ɓuraguzai.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya sa doka a Kano ana dab da fara zaɓen ƙananan hukumomi

Gini ya rufto a Abuja
Gini ya rufto kan mutane a Abuja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa ginin ya ruguje ne a ranar Asabar, 26 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gini ya danne mutane a Abuja

Mutanen da ke wajen sun buƙaci a kawo agajin gaggawa domin taimakawa wajen ceto mutanen da ginin ya rufta musu.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa aƙalla mutane 40 ne suka maƙale a ginin, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Aƙalla mutane 40 ne suka maƙale a wani gini da ya rufta a unguwar Sabon Lugbe da ke babban birnin tarayya Abuja. Mutane suna ƙarƙashin ɓuraguzan ginin. 
"Gini ne da ake ginawa. Muna kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su zo a ceto mutanen da suka maƙale a nan."

- Wani ganau

Gini ya rufta kan mutane a Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa an ceto mutane biyu da ransu daga ƙasan wani gini da ya rufta kansu a wani rukunin gidaje na Prince and Princess da ke gundumar Gudu, babban birnin tarayya Abuja.

Mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa ta Abuja (FEMD), Nkechi Isa ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, 29 ga watan Yunin 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng