Wata Jihar Arewa Ta Sake Ficewa daga Shari'ar Neman Rusa Hukumar EFCC
- Gwamnatin juhar Jigawa ta sanar da ficewarta daga ƙarar da ke neman a soke hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC)
- Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar ya sanar da janyewar a ranar Asabar, 26 ga watan Oktoban 2024
- Bello Abdulkadir-Fanini ya bayyana cewa jihar ta shigar da buƙatar neman janyewa daga ƙarar ne a ranar 24 ga watan Oktoban 2024 a Kotun Ƙoli
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Jigawa - Gwamnatin Jigawa ta bayyana matsayarta kan ƙarar da wasu gwamnoni suka shigar ta neman a rusa hukumar EFCC.
Gwamnatin ta ce ta janye daga ƙarar wacce ke ƙalubalantar dokokin da suka kafa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) a Kotun Ƙoli.
Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar, Bello Abdulkadir-Fanini ne ya sanar da janyewar a taron manema labarai a birnin Dutse ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigawa ta janye daga ƙarar EFCC
Bello Abdulkadir-Fanini ya ce an shigar da buƙatar janyewar jihar daga ƙarar ne a ranar 24 ga watan Oktoban 2024, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
"Bari a daidai nan gaɓar na sanar da cewa gwamnatin jihar Jigawa ta janye daga shari'ar Antoni Janar na Kogi VS Antoni Janar na tarayya mai lamba SC/CV/178/2023), wacce ke a Kotun Ƙoli."
"Buƙatar janyewar wacce na sanyawa hannu an shigar da ita a Abuja a ranar, 24 ga watan Oktoban 2024."
- Bello Abdulkadir-Fanini
Sai dai kwamishinan shari'ar bai bayyana dalilin da ya sa jihar ta janye daga ƙarar ba.
Karanta wasu labaran kan EFCC
- Kotun Koli ta dauki mataki kan karar da ke neman rusa hukumar EFCC
- EFCC ta dura gidan rediyo ana tsaka da watsa shiri kai tsaye, NBC ta dauki zafi
- 'Ya ƙware': Yadda ɗan shekara 17 ya yi kutse a na'urar shugaban hukumar EFCC
Gwamnan Zamfara baya tsoron EFCC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa ba ya tsoron hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC).
A cewar Gwamna Dauda, ya kamata mutanen da aka zaɓa a kan muƙaman shugabanci su kasance masu riƙon amana da gaskiya.
Asali: Legit.ng