Yadda Masu Caji Ke Samun Alheri Sakamakon Lalacewar Wutar Lantarki a Jihohin Arewa

Yadda Masu Caji Ke Samun Alheri Sakamakon Lalacewar Wutar Lantarki a Jihohin Arewa

  • Mutuwar wani tashin wani, kasuwar masu cajin waya ta bude sakamkon rashin wutar lantarki a wasu jihohin Arewa
  • Legit Hausa ta ziyarci wasu masu caji a jihar Katsina inda ta taras da wayoyi masu dumbin yawa da aka kai caji
  • A ƴan kwanakin nan Najeriya na fama da matsalar lalacewar layin raraba wuta, kamfanin TCN ya ce yana iya bakin ƙoƙarinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Yayin da ƴan Najeriya ke kokawa kan lalacewar wutar lantarki, su kuma masu caji yanzu ne kasuwarsu ta buɗe.

Wani mai shagon cajin waya a Unguwar Rogo da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato, ya ce kasuwa ta buɗe sosai saboda rashin wuta a wasu jihohi.

Kara karanta wannan

Kaico: Ɗalibai 2 sun mutu a wani harin kwantan ɓauna, mutane sun shiga jimami

Wurin masu caji.
Kasuwar masu caji ta buɗe da aka samu matsalar wutar lantarki a Arewa
Asali: Original

A wani rahoto da Daily Trust ta tattara, mutumin mai suna Auwal Bayya, ya ce a yanzu yana samun kuɗin da yake iya ɗaukar ɗawainiyar iyalinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Galibin jihohin Arewa na fama da rashin wuta a yanzu haka sakamakon lalacewar layin wutar lantarki mai ƙarfin 330KV a tsakanin Makurɗi a Benuwai da Enugu.

"Kasuwa ta ɓuɗe mana" - Auwal

Da yake jawabi kan yadda kasuwa ta buɗe masa, mai cajin ya ce dama haka rayuwa ta ke, a lokacin da wani ke dariya, wani na can rayuwa ta masa ƙunci.

Auwal ya ce:

"Rayuwa kenan, a lokacin da wani ke dariya wani kuma kuka yake, ni dai Alhamduillah a yanzu ina samun kuɗin ciyar da iyali na, amma a da ba kowa ke kawo mani caji ba.
"Tun da wuta ta lalace mutane suka fara tururuwar kawo mani cajin wayoyi, ina caza waya akalla 100 kowace rana da kwamfutoci, cociloli da sauransu.

Kara karanta wannan

Matsalar lantarki: TCN ya fadawa yan Arewa gaskiya kan halin da za a shiga

"Gaskiya ina cikin masu amfana da wannan yanayin na rashin wuta amma duk da haka ina tausayawa ƴan Najeriya."

'Muna caza wayoyi akalla 200 a rana'

Wakilin Legit Hausa ta ziyarci wurin wani caji a garin Dabai da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a Katsina kuma ya ga irin wayoyin da ake tarawa saboda rashin wuta.

Naziru mai caji ya shaidawa wakilinmu cewa a yanzu sun samun wayoyi akalla 200 a kowace rana, wasu kuma batiri suke kawowa caji.

"Rashin wuta ba alheri ba ne amma mu sai dai mu godewa Allah kasuwa ta buɗe, duk da haka mun fatan a gyara wutar domin kowa ya samu sauki," in ji sh.

TCN ta gano asalin matsalar da aka samu

A wani labarin kuma kamfanin TCN ya bayar da rahoton lalacewar wutar lantarki a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya.

Manajan hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah ya bayyana cewa wasu layukan wuta da ke kan tashar Ugwaji-Apir ne suka samu matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262