Yan Majalisa Sun Amince da Shirin Karya Farashin Abinci

Yan Majalisa Sun Amince da Shirin Karya Farashin Abinci

  • Yan majalisar dokokin jihar Sokoto sun amince da shirin gwamna Ahmed Aliyu na karya farashin kayan abinci a sassan jihar
  • Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu ne ya fara karya farashin abinci a jihar Sokoto domin rage radadin tsadar rayuwa ga talakawa
  • Goyon bayan yan majalisar dokokin zai ba gwamnan jihar damar cigaba da karya farashin abinci ga talakawan jihar Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Gwamna Ahmed Aliyu ya samu goyon bayan yan majalisar dokokin Sokoto domin cigaba da karya farashin abinci.

Ana san ran cewa talakawan Sokoto daga dukkan mazabun jihar za su samu sauki daga tsadar abinci da ake fama da ita a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Haraji a wuraren ibada: Malaman addini sun dura kan gwamna

Sokoto
Yan majalisar Sokoto sun yarda da karya farashin abinci. Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa dan majalisar jihar mai wakiltar Yabo ne ya fara goyon bayan kudirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta amince da karya farashin abinci

Majalisar dokokin jihar Sokoto ta goyi bayan gwamna Ahmed Aliyu na cigaba da sayar da abinci ga talakawa a farashi mai rahusa.

Majalisar dokokin ta goyi bayansa ne domin cigaba da samar da abinci mai sauki ga talakawa bayan ya fara shirin a baya.

Dalilin sauke farashin abinci a Sokoto

Dan majalisa mai wakiltar Yabo, Abubakar Shehu ya ce suna sane da yadda al'umma suke fama da wahalar rayuwa da matsin tattalin arziki.

Hon. Abubakar Shehu ya kara da cewa mutane da dama ba su samun damar cin abinci saboda yanayin yau kuma saboda haka ne suka goyi bayan shirin.

Yadda farashi zai kasance a Sokoto

Hon. Abubakar Shehu ya ce a yadda aka fara shirin, an karya farashin buhun shinkafa da ake sayarwa N65,000 zuwa N70,00 a kan N35,700 wanda haka ake fata shirin ya cigaba.

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ruwa ya karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

Daga karshe, shugaban majalisar, Tukur Bala ya karanta kudirin kuma ya samu goyon bayan dukkan yan majalisar dokokin jihar.

Za a karya farashin abinci a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta shirya domin kafa rumbunan sauki saboda karya farashin kayan masarufi.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa zai kafa rumbun sauki a dukkan kananan hukumomin Katsina saboda karya farashin abinci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng