Hadimin Gwamnan Kano Ya Yi Rashi, Baban Ɗansa Ya Rasu a Ƙasar Indiya
- Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya yi rashin babban ɗansa, Sadiq Modibbo
- Sanusi ya bayyana cewa Sadiq ya rasu ne bayan fama da ciwon sikila kuma za a dawo da shi gida domin jana'iza
- Hadimim gwamnan ya ce Sadiq, ɗan shekara 15 a duniya yaron kirki ne mai son zumunci kuma yana da biyayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya yi rashin babban ɗansa, Sadiq Modibbo Bature.
Sadiq, ɗan kimanin shekara 15 a duniya ya rasu ne bayan an masa tiyata a ƙasar Indiya ranar Alhamis.
Babban ɗan kakakin gwamnan Kano ya rasu
Kakakin gwamnan Kano ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook jiya Alhamis da daddare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayin ya sha fama da ciwon sikila tun da aka haife shi zuwa yanzu da ya koma ga mahallinsa.
Da yake sanar da rasuwar a shafinsa, Sanusi Bature ya bayyana cewa Sadiq shi ne babban ɗansa kuma ya rasu ne bayan an masa tiyata a wani asibitin Indiya.
Sanusi Dawakin Tofa ya sanar da jana'iza
“Da safiyar nan Allah ya yiwa ɗana na farko Sadiq (Modibbo) Bature rasuwa, yana ɗan shekara 15, yaron kirki, mai son mutane da biyayya ga iyaye, yana da son zumunci."
"A tsawon rayuwarsa, Modibbo ya yi fama da ciwon sikila wanda aka yi masa dashen ɓargo a cikin watan nan a wani asibiti a Indiya.
Sai dai ya rasu ne sakamakon wata matsala da ya samu a kwakwalwa bayan tiyatar. Za a dawo da gawarsa gida nan da ‘yan kwanaki domin yi masa jana'iza a garinmu, Dawakin-Tofa."
- Sanusi Bature.
Hadimin gwamnan ya ce za a sanar da lokacin da za yi jana'iza bayan gawarsa ta isa gida.
Tsohon shugaban INEC ya rasu a Amurka
A wani labarin kuma, an shiga jimami bayan rasuwar tsohon shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Farfesa Humphrey Nwosu a Amurka.
Farfesa Nwosu ya rasu ne bayan fama da jinya a birnin Virginia da ke kasar Amurka yana da shekaru 83 a duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng