'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Manoma, Sun Sace Kayan Abinci

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Manoma, Sun Sace Kayan Abinci

  • Ƴan bindiga sun kai hari a wasu ƙauyuka biyar na ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna a Arewa maso Yamma
  • Ƴan bindigan sun yi awon gaba da wasu manoma guda huɗu tare da sace kayan abinci a harin da suka kai
  • Majiyoyi sun ce ƴan bindigan sun kai harin ne jim kaɗan bayan sojojin da ke aikin sintiri sun fice daga ƙauyukan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da wasu manoma guda huɗu a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun kuma sace kayan abinci a harin da suka kai a ƙauyen Arikon da ke ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun sace manoma a Kaduna
'Yan bindiga sun sace manoma da kayan abinci a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ce wani shugaban al’ummar yankin ya tabbatar mata da cewa lamarin ya auku ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 5:12 na yamma.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka matafiya, sun yi awon gaba da manoma a Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Ya ce ƴan bindigan sun yi awon gaba da biyu daga cikin manoman ne a ƙauyen Impi da ke makwabtaka da su kafin su wuce zuwa Arikon inda suka sace wani mutum da wata mata da suke dawowa daga gona.

Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun shiga wani rumbun ajiye kayan amfanin gona inda suka ɗauki buhun shinkafar gida da doya mai yawa.

"Ƴan bindigan waɗanda suka zo a kan babura sun fasa wani rumbu a ƙauyen Impi da ke da nisan kilomita daga Arikon inda suka sace buhun shinkafa da doya."

- Wani shugaban al'umma

Shugaban al’ummar ya ce lamarin ya auku ne jim kaɗan bayan da sojojin da ke sintiri suka bar ƙauyukan guda biyu.

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur ba kan lamarin.

Kara karanta wannan

Wani ɗan bindiga ya tona asiri, ya faɗi yadda suke amfani da kudin fansa

Yaran da za su iya zama ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya ya nuna danuwa kan yawan ƙananan yara masu gararamba a gari waɗanda ba su zuwa makaranta.

Sanata Godswill Akpabio ya ce alkaluma sun nuna akwai yara miliyan 20 da ba su zuwa makaranta a faɗin ƙasar nan, yana mai cewa za su iya zama ƴan bindiga nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng