An yi Nasarar Gano Matsalar Lantarki a Arewa, TCN Ya yi Karin Haske

An yi Nasarar Gano Matsalar Lantarki a Arewa, TCN Ya yi Karin Haske

  • Kamfanin rarraba lantarki na kasa (TCN) ya gano musabbabin rasa wutar lantarkin a wasu garuruwan Arewacin Najeriya
  • TCN ya ce zai fara aiki tuƙuru domin magance matsalar kuma ya bayyana kayan aiki da ya ke bukata domin warware damuwar
  • Tun a Litinin wutar lantarki ta dauke a sassan Arewa, hakan ya jefa al'umma cikin damuwa, ya shafi ayyuka na yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Kamfanin rarraba wuta na kasa (TCN) ya yi nasarar gano matsalar lantarki da ta jefa Arewacin Najeriya cikin duhu.

An ruwaito cewa a yammacin ranar Laraba injiniyoyin TCN suka gano matsalar a wani yanki na jihar Benue.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ɗauko Ministan Buhari, ya naɗa shi a muƙami bayan korar ministoci

Lantarki
TCN ya fara gyara wutar Arewa. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Kamfanin TCN ne ya bayyana halin da ake ciki a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya samu wutar lantarki a Arewa?

Kamfanin TCN ya bayyana cewa ya gano wata matsala da aka samu a kan layin wuta na Ugwuaji-Apir 330kV.

TCN ya gano yadda layin wutar lantarki ya lalace ne a ranar Laraba da misalin karfe 5:00 na yamma a yankin Igumale na jihar Benue.

TCN ya fara gyara wutar lantarki a Arewa

Tun bayan gano matsalar, TCN ya fara ƙoƙarin tanadar kayan aiki da za su isa wajen domin gyara a kan lokaci.

Sai dai TCN ya bayyana cewa wajen na cikin daji mai itace da caɓali saboda haka zai bukaci mota kirar bulldozer da wasu kayan aiki daga ofishinsa na Enugu zuwa wajen.

Kara karanta wannan

Duk da Dala ta haura N1600, IMF ya yabi kokarin CBN, ya yi ikirarin Naira ta mike

TCN ya ba mutane hakuri kan lantarki

Kamfanin TCN ya ce zai cigaba da ƙoƙarin magance matsalolin lantarki da suka faru da waɗanda za su faru a kan lokaci.

A karkashin haka, ya yi kira ga yan Najeriya, gwamnati da kamfanoni kan su cigaba da hakuri har a kammala gyaran wutar.

An bukaci korar shugaban TCN

A wani rahoton, kun ji cewa matasa sun buƙaci a kori ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu da shugaban kamfanin rarraba wuta na ƙasa TCN.

Ƙungiyar matasan NYTGG ta ce akwai sakaci a yawan lalacewar babban layin lantarki wanda ya samu matsala sau uku a mako guda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng