Rashin Tsaro: Gwamnati Za Ta Karbo Rancen $600m, a Sayo Jiragen Yaki
- Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa za ta ranto Dala miliyan 600 domin sayo manyan jiragen yaki samfurin Italiya
- Tun a zamanin tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari, gwamnatin kasar nan ta bayyana sha'awar mallakar jiragen yakin
- Ana sa ran idan gwamnati ta yi nasarar samun jiragen, za a fara kai hari maboyar yan ta'addan da su ka addabi sassan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na sayo manyan jiragen yaki kirar Italiya M-346 domin kakkabe yan ta'adda.
Wannan na zuwa ne yayin da masana tsaro ke ganin sojojin kasar nan na bukatar kayan aikin zamani domin yaki da yan ta'adda masu manyan makamai a Arewa.
BBC Hausa ta wallafa cewa Najeriya ta fara kokarin mallakar samfurin jiragen yakin tun a gwamnatin baya ta Muhammau Buhari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsaro: Za a sayo jiragen yaki
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa za ta karbo rancen Dala miliyan 600 domin sayo manyan jiragen yaki da za a yi amfani da su wajen kai wa yan ta'adda hari.
Batun na zuwa a lokacin da gwamnatin tarayya ta ba dakarun sojin kasar nan umarnin kakkabe yan ta'adda daga maboyarsu a Arewa maso Yamma.
Ana shirin dawo da tsaro Najeriya
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya za su yi amfani da jiragen M-346 wajen fatattakar yan ta'adda.
Ana fatan da zarar an yi nasarar karbo rancen, za a sayo jiragen da sojojin za su fara amfani da su a farkon shekarar 2025 mai kamawa.
Rundunar tsaro ta gargadi sojoji
A wani labarin kun ji cewa rundunar tsaron kasar nan ta ja kunnen yan ta'adda da ke cin karensu babu babbaka, musamman a Arewa maso Yamma da cewa su gaggauta zubar da makamansu.
Shugaban rundunar Fansar Yamma, Manjo Janar Oluyinka Soyele ne ya tura gargadin a lokacin da ya kammala ganawa da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal kan tsaro a yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng