Sarki Sanusi II Zai Nada Babban Dansa Sarautar Ciroman Kano, Bayanai Sun Fito
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zai nadawa babban dansa sarautar Ciroman Kano a ranar Juma'a, 25 ga Oktoba
- An rahoto cewa mahaifin Sarkin Kano na yanzu, Ambasada Aminu Sanusi, ya rike mukamin har zuwa rasuwarsa a 1990
- Baya ga DSP Aminu Lamido Sanusi, an kuma rahoto cewa Mai martaba zai nadawa wasu mutane tara sarauta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya kammala shirye-shiryen yiwa babban dansa nadin sarautar Ciroman Kano.
Rahoto ya nuna cewa yariman masarauta (babban dan sarki) ko kuma mai jiran gadon sarauta ne ake yiwa nadin sarautar 'Ciroma.'

Source: Twitter
Sanusi II zai yiwa dansa sarautar 'Ciroma'
Mahaifin sarkin Kano na yanzu, Ambasada Aminu Sanusi, ya rike mukamin har zuwa rasuwarsa a shekarun 1990 a cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanda ya rike mukamin na karshe shi ne Alhaji Nasiru Ado Bayero, wanda aka nada Sarkin Bichi a shekarar 2020.
Idan za a tuna, gwamnatin Abba Kabir Yusuf tube rawaninsa bayan shekaru hudu a kan mulki da aka soke masarautu.
Za a yi wa dan Sanusi II na farko, Aminu Lamido Sanusi, wanda dan sanda ne mai mukamin DSP nadin sarautar ne tare da wasu mutum tara a ranar Juma’a, 25 ga Nuwamba, 2024.
Sanusi II zai yi wa mutane 10 sarauta
Ga jerin wadanda Sarki Sanusi II zai yiwa nadin sarauta a ranar Juma'a mai zuwa:
- DSP Aminu Lamido Sanusi - Chiroman Kano
- Mahmud Aminu Yusufu - Mai Unguwar Mundubawa
- Dr. Abubakar Aminu Sanusi (Wambai) - Dan Madami
- Arch. Ali Muktar - Sa'in Kano
- Sarki Yusuf Bayero - 'Yan Daka
- Abdullahi Idris Bayero - Fagacin Kano
- Ado Abdullahi Aminu - Kaigaman Kano
- Idris Sanusi - Sarkin Sullubawa
- Mansur Isa Bayero - Sarkin Kudu
- Abdullahi Sarki Mohammed - Sarkin Yamma
Dan Sarki Sanusi II ya auri 'yar sanata
A wani labarin, mun ruwaito cewa kwanaki kadan da dawowar Sarki kan sarautar Kano, dansa, Ashraf zai auri 'yar Sanata Sulaiman Nazif.
A ranar 2 ga watan Agustan wannar shekarar ne Sarki Muhammadu Sanusi II aurar Ashraf Lamido ga masoyiyarsa mai suna Sultana Nazif.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

