Ambaliyar Ruwa: An Shiga Jimami bayan Mutane da Dama Sun Rasa Matsugunansu
- Mutane masu yawa sun rasa matsugunansu bayan an samu ambaliyar ruwa a ƙaramar hukumar Obio/Akpor ta jihar Rivers
- Jama'a sun koka da cewa ambaliyar ruwan ta tilasta musu barin gidajensu bayan macizai sun mamaye inda suke rayuwa
- Mutanen da ke yankin Rumaholu-Nkpolu sun yi kira ga gwamnatin jihar kan ta gina musu magudanun ruwa domin gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Sama da iyalai 200 ne a yankin Rumaholu-Nkpolu da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a jihar Rivers suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa.
Hakan dai ya faru ne yayin da mazauna garin suka ce macizai sun mamaye gidajensu sakamakon mummunar ambaliyar ruwan.

Asali: Original
Ambaliya ta yi ɓarna a Rivers
Mazauna yankin sun shaidawa jaridar The Punch cewa sun fara fuskantar irin wannan ambaliya ne a shekarar 2017 bayan da wasu mutane suka gina gidaje a magudanun ruwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗaya daga cikin mutanen da lamarin ya shafa mai suna Thomas, ya ce a duk lokacin da ambaliyar ta afku, za su shafe kimanin watanni bakwai ba sa cikin gidajensu duk shekara suna jiran ruwan ya janye.
Ya bayyana cewa a wannan shekarar sun gudu daga gidajensu bayan sun ga macizai na fitowa daga cikin ruwan.
"Idan yanzu na kai ku cikin kowane gida da aka fita aka bari, za a samu macizai kusan guda shida."
"A cikin dare, idan babu fitila musamman yayin da ake saukowa daga kan matakala, za a ga macizai. Wani lokaci, kusan muna taka macizai, shi ya sa yawancin mu suka gudu."
- Thomas
Jama'a sun miƙa kokensu ga gwamnati
Wata mata da ta nemi a sakaya sunanta ta yi kira ga gwamnatin jihar Rivers da ta kawo musu ɗauki ta hanyar gina magudanun ruwa a yankin.
"Muna kira ga gwamnati da ta gina mana magudunan ruwa. Sai mun yi amfani da kwale-kwale sannan muke zuwa gidajenmu."
- Wata mata
Ambaliyar ruwa ta lalata gonaki
A wani labarin kuma, kun ji cewa ambaliyar ruwa ta lalata amfanin gonakin al'umma a karamar hukumar Argungu da wasu yankunan da dama a jihohin Kebbi da Neja.
Shugaban sashin hulɗa da jama’a na Hukumar bunƙasa wutar lantarki ta ƙasa (N-HYPPADEC), Nura Wakili ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 27 ga watan Agustan 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng